’Yan sanda sun cafke wasu ’yan uwan juna su biyu kan yi wa wata karamar yarinya mai shekara hudu tare.
An gurfanar da su ne a gaban Kotun Majistare da ke Yaba a Jihar Legas kan yi wa ’yar makwabcinsu fyade.
- Yajin aiki: ASUU ta caccaki dalibai kan juya mata baya
- Musulunci ya bai wa mata damar samun ilimi da aiki —Taliban
’Yan sanda sun tsare su ne bayan wata kungiya jinkai, Landa’s Bethel Foundation, ta aike wa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar takardar korafi kan lalata karamar yarinyar da aka yi.
Kungiyar ta bayyana cewa wadanda ake zargin sun yaudari yarinyar ce zuwa cikin gidansu, inda kowanne daga cikinsu ya yi lalata da ita.
Sai dai mai gabatar da kara, Thomas Nurudeen, bai bayyana sunayensu ba, saboda a cewar kananan yara ne mau shekaru 10 da kuma 15.
Alkalin kotun, P. E. Nwaka, ya ba da umarnin tsare su a gidan kangararrun yara tare da mika takardar zargin su ga Sashen Shari’an Gwamnatin Jihar Legas, kafin ya dage sauraren shari’ar.