Wasu mabiya Kungiyar Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), wato Izala, bangaren Jos, sun yi Sallar Idin Karamar Sallah sabanin umarnin Sarkin Musulmi na cika azumi 30.
Mabiyan Izalar, reshen Goron Namaye, Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, sun gudanar da Sallar Idi ne a ranar Laraba bisa hujjar ganin watan Shawwal a wurare daban-daban, a Najeriya a cewarsu.
- Dalilin da Sheikh Dahiru Bauchi ya gudanar da Idin Karamar Sallah
- Kungiyar Dattawan Arewa ta bukaci Majalisa ta tsige Buhari
- Kungiyar Mata ’yan jarida ta yi taron yi wa kasa addu’a a Gombe
Ranar Talata da dare, Sarkin Musulmi ya ba da umarnin a yi azumi Ranar Laraba domin cika adadin watan Ramadan kwana 30 saboda rashin ganin wata a ranar duban farkon.
Amma bayan saukowa daga sallar idi a ranar, wani mabiyin Izala bangaren Jos a Gordon Namaye, mai suna Saidu Abdullahi Goran Namaye ya wallafa hotunan a shafinsa na Facebook.
Sa’idu ya ce sun yi Sallar Idin a safiyar Laraba ce saboda sun samu tabbacin ganin watan Shawwal.
Shi ma jagora a Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi da dubban mabiyansa sun gabatar da ta su Idin a garin Bauchi.
Shekara biyu a jere ana takaddama
Shekara ta biyu ke nan a jere ake samu wannan babbar matsala, in Kungiyoyin Addini ke bijire wa umarnin Sarkin Musulmi, na cika azumi zuwa 30.
Irin haka ta faru a shekarar 2020, inda a waccan shekarar ma Sheikh Dahiru Bauchi ya jagoranci sallar idi a ranar a Sarkin Musulmi ya ba da ce a yi azumi na 30.
Tun kafin ranar 29 ga watan Ramadan, wadda ita ce ranar duban farko na watan Karamar Sallah, masana suka fara hasashen cewa da wuya jinjirin watan ya tsayu a ranar 29 ga watan.
Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce inda wasu ke zargin son zuciya da neman tursasa wa mutane cika azumin bana 30.
Sanarwar da hadimi kan harkokin addini kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, ya fitar ta ce a duk fadin Najeriya ba a samu labarin ganin watan Shawwal ba, saboda haka Alhamis ce za ta kasance ranar Karamar Sallah bayan cika kwanaki 30.