Wata Kotun Majistare da ke Osogbo, a Jihar Osun ta bayar da umurnin garkame wasu matsafa biyu tare da wasu mutum hudu a gidan yari kan zargin kashe wani mutum mai shekara 35 domin yin tsafi.
Dan sanda mai gabatar da kara, ASP John Idoko, ya shaida wa kotun cewa matsafan, sun hada baki ne da sauran mutanen suka kashe mutumin sannan suka yanke wasu sassan jikinsa.
- Jama’a sun kona motar kwastam da ta kashe mutane a Jibiya
- An dakatar da rigakafin Coronavirus saboda wasu kura-kurai da aka gano
Idoko ya bayyana wa kotun cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne da misalin karfe 9:30 na dare, a ranar 24 ga Mayu, 2021, a Ikirun, Jihar Osun..
A cewarsa, hakan laifi ne karkashin sashe na 324, 319 (1), 517, 242 da 329A na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Osun na 2002.
Sauran mutum hudun sun musanta zargin da ake musu, kuma lauyansu, Shakiru Kabiru, ya nemi kotun ta ba da belinsu.
Sai dai gabatar da kara ya ki amincewa bisa hujjar cewa kashe-kashe da sauran manyan laifuffuka sun yi yawa a jihar, inda ya ce idan aka ba da su beli, hakan zai bude kofar neman beli ga sauran masu aikata irin laifin.
Alkalin kotun O. A. Daramola ya sa tsare wadanda ake zargin a Gidan Yari na Ilesa, sannan ya ba da umarnin mika takardun binciken wanda ake zargin zuwa sashen bincike na kotun.