✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wasu masu coronavirus a Osun sun tsere bayan killace su

Wasu mutum shida da aka tabbatar suna dauke da coronavirus sun tsere daga cibiyar da aka killace su a jihar Osun. Bayanai sun tabbatar da…

Wasu mutum shida da aka tabbatar suna dauke da coronavirus sun tsere daga cibiyar da aka killace su a jihar Osun.

Bayanai sun tabbatar da cewa mutanen da suka tsere suna cikin ayarin mutanen nan ‘yan asalin ‘yankin Ejigbo a jihar Osun wadanda  da suka dawo daga kasar Ivory Coast.

Wani jami’in gwamnatin jihar ta Osun ya tabbatar wa jaridar Daily Trust faruwar lamarin, yana mai cewa mahukunta na neman mutanen ruwa a jallo.

A makon jiya ne dai ayarin da wadannan mutane 127 ‘yan asalin yankin Ejigbo ke ciki ya dawo daga Ivory Coast, kuma bayan an kebe su an yi masu gwaji aka tabbatar mutum 12 na dauke da cutar.

Gano mutanen ne ya sa adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar ya yi tashin gwauron zabi a lokaci guda daga biyu zuwa 14.