✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu daga cikin Mu’ujizojin Alkur’ani (1)

Manzannin da Allah (SWT) Ya aiko tun daga Annabi Nuhu (AS) zuwa kan Annabinmu Muhammad (SAW) kowa da irin baiwar da Allah kan zaba Ya…

Manzannin da Allah (SWT) Ya aiko tun daga Annabi Nuhu (AS) zuwa kan Annabinmu Muhammad (SAW) kowa da irin baiwar da Allah kan zaba Ya kebance shi da ita, don ya zamo darasi da kuma nuni ga mutanensa cewa daga Allah yake. Amma kowane Manzo mu’ujizarsa tana shudewa ya zamo sai labarinta, amma ban da Alkur’ani.
Ga misalai kamar haka:
1.  Annabi Sulaiman (AS) yana da mu’ujizozi masu yawa, daga ciki ya yi magana da tsuntsaye har da tururuwa kamar yadda ya zo cikin Alkur’ani a Suratun Namli aya ta 17:
“Kuma aka tattaro wa Sulaiman rundunoninsa daga aljanu da mutane da tsuntsaye, kuma aka kange su cikin ayari. Har lokacin da suka iso kan rafin tururuwa, sai wata tururuwa ta ce, “Ya ku jama’ar tururuwa! Ku shiga gidajenku kada Sulaiman da rundunoninsa su tattake ku, alhali ba su sani ba. Sai ya yi murmushi yana mai dariya daga maganarta, kuma ya ce ya Ubangijina Ka cusa mini godiya ga ni’imarKa wadda ka ni’imta gare ni…”  (27:17).
Haka kuma Annabi Sulaiman ya yi magana da Alhuda-huda (wato daya daga cikin tsuntsayen da ke cikin ayarinsa) kamar haka:
“Sai ya zauna ba da nisa ba (wato Alhuda-hudan) sannan ya ce, “Na san abin da ba ka sani ba, kuma na zo maka daga Saba’i da wani labari tabbatacce.” (27:22).
Bayan Annabi Sulaiman ya saurare shi sai ya ce:
“Za mu duba, shin ka yi gaskiya ne ko kuwa ka kasance daga makaryata, ka tafi da takardata wannan, sannan kuma ka jefa ta zuwa gare su…” (27:27-28).
2. Annabi Musa (AS): Cikin mu’ujizozinsa yakan jefa sandarsa ta zamo macijiya, ko ya saka tafin hannunsa a hammata ya fitar da shi yana haske. Wannan magana ta tabbata a cikin Alkur’ani. Cikin Suratul Shu’ara’i, Allah Ya ce:
“Sai ya jefa sandarsa, sai ga ta ta zama kumurci bayyananne, kuma ya fitar da hannunsa sai ga shi ya zama fari ga masu kallo.”  (26:32-33).
3. Annabi Isa (AS): Cikin nasa mu’ujizojin yakan rayar da matattu, yana warkar da makaho da mai albaras da sauransu. Tabbacin hakan kuwa ya zo alal misali cikin Suratu Ali Imrana kamar haka:
“Kuma (Ya saka shi) manzo zuwa Bani Isra’ila (yana mai cewa), “Lallai ne hakika na zo muku da wata aya daga Ubangijinku, lallai ne ina halitta muku daga laka kamar siffar tsuntsu, sannan in yi huri a cikinsa, sai ya kasance tsuntsu da izinin Allah, kuma ina warkar da wanda aka haifa makaho da kuturu, kuma ina rayar da matattu, da izinin Allah. Kuma ina fada muku abin da kuke ci da abin da kuke ajiyewa a cikin gidajenku. Lallai ne a cikin wannan akwai aya a gare ku, idan kun kasance masu yin imani.” (3:49).
4. Annabi Muhammadu (SAW): Duk wadannan  kadan ke nan daga cikin mu’ujizozin da Allah Ya yi wa wasu daga cikin Manzanni da AnnabawanSa. Sai dai wadannan manzanni littafin da aka aiko su da shi ba shi ne mu’ujizarsu ba, amma Annabinmu Muhammadu (SAW), littafin da aka aiko shi da shi zuwa gare mu shi ne mu’ujizarsa. Abin da yake cikin Alkur’ani ba ya tsufa, ko a ce yayinsa ya wuce, ko zamani ya bijiro da wani sabon abu da babu a cikin Alkur’ani.
Alkur’ani littafi ne gagara-badau mai cike da hikimomi da ilimin abubuwan da suka fi karfin a ce kirkirarsa aka yi, ko a ce ba daga Allah yake ba. Cikinsa akwai umarni da hani da tsoratarwa da bushara da gargadi da kwadaitarwa da ba da labarin abin da ya wuce ko wanda ake ciki da lokaci mai zuwa. Ga shi da dadin sauraro da saukin hadda da kuma saukin fahimtar ma’anarsa. Don haka Allah Ya kalubalanci dukkan masu shakkar Alkur’ani a matakai da dama:
“Kuma, idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka saukar ga bawanMu, to ku zo da sura guda na daga misalinsa, kuma ku kirawo shaidunku baicin Allah, idan kun kasance masu gaskiya.” (2:23).
“Ko suna cewa ya kirkiro shi ne? Ka ce to ku zo da sura guda misalinsa, kuma ku kirayi duk wanda za ku iya kira bayan Allah, idan kun kasance masu gaskiya.”  (Suratu Yunus aya ta 38)
“Ko suna cewa ya kirkiro shi ne? Ka ce sai ku zo da surori goma misalinsa kirkirarru, kuma ku kirayi wanda kuke iyawa, baicin Allah idan kun kasance masu gaskiya.” (Suratu Hud aya ta 13).
“Ka ce: “Lallai ne da mutane da aljanu za su taru a kan su zo da misalin Alkur’ani, ba za su zo da misalinsa ba kuma ko da sashinsu ya kasance mataimaki ga sashi.” (17:88).
Wani abin dubawa shi ne, Annabi Muhammadu (SAW) wanda shi aka saukar wa wannan littafi a matsayin dan aiken Allah zuwa ga al’ummarsa, bai iya karatu da rubutu ba, balle a ce shi ya kirkiro, ko ya ji daga maganganun magabata, ko masu ilimin zamaninsa Allah (SWT) Ya ce:
“Kuma ba ka kasance kana karanta wani littafi ba gabaninsa, kuma ba ka rubutunsa da hannuwanka, da ka yi hakan kuwa da masu barna sun yi shakka.” (Suratul Ankabut aya ta 48).
Shi Annabi Muhammad (SAW) bai yi yawo ko’ina ba cikin fadin duniya, kafin zuwan sakon Allah gare shi. Yana nan zaune cikin kasar da take sahara, amma Allah Ya zabe shi Ya aiko masa da wannan littafi. Kuma Annabi (SAW) ba ya da wani malami da za a ce daga wurinsa ya samu hikimar Alkur’ani. Allah (SWT) Yana cewa:
 “Shin ba su kula da Alkur’ani, da ya kasance daga wanin Allah ai da an samu saba wa juna mai yawa a cikinsa.” (4:82).
Alkur’ani mai girma, saukarsa ta gabaci zamanin nan da muke ciki, amma duk abin da ingantaccen ilimin kimiyyar zamani ya zo da shi tabbatacce, to Alkur’ani ya rigaye shi. Wannan na daga cikin mu’ujizar Alkur’ani. Dubi misalai kamar haka:
1.    Ilimin Halitta: Bayani a kan halittar dan Adam da dabbobi da tsirrai, wanda har yanzu ake ta yin bincike a kansu. Game da halittar dan Adam, Allah (SWT) Ya ce a cikin Suratul Muminun:
“Kuma lallai ne, hakika Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga laka, sannan Muka sanya shi digon maniyyi a cikin matabbata matsattsiya, sannan Muka halitta shi gudan jini, sannan Muka halitta gudan tsoka, sannan Muka halitta kasusuwa, sannan Muka tufatar da kasusuwan da wani nama, sannan Muka kaga shi wata halitta daban….”  (23:12,13,14).

Malam Aliyu Muhammad Sa’idu Gamawa
karamar Hukumar Gamawa Jihar Bauchi
08035829071