Hamdala da taslimi:
Ya ku ’yan uwa Musulmi!
Dukkanmu mun san cewa, addinin Musulunci addini ne na rayuwa gaba daya. Yin addini bai tsaya ga yin Sallah ko Azumi ko Hajji ba. Mika wuya ga Allah a sha’anin rayuwa gaba daya shi ne Musulunci. Wannan ya sa a makon jiya muka mika sako zuwa ga ’yan kasuwa Musulmi a matsayinsu na wadanda Allah Ya shar’anta wa dokoki a cikin wannan harka tasu. Kamar haka ne a yau muke son gabatar da wasu nasihohi da shawarwari ga wadanda sha’anin siyasa ya shafa; masu zabe da wadanda ake zaba, jami’an tsaro da malaman zabe da duk masu ruwa da tsaki a cikin wannan sha’ani.
Babu shakka, siyasa a yau ta hadu da miyagun abubuwa. Da zarar aka ambaci sunan siyasa tunanin mutane zai je ga yaudara da ha’inci da munafunci da rashin mutunci. Gogaggen dan siyasa a yau shi ne wanda ya kware wajen zamba da cin mutunci. Shi ne, wanda ya iya bata sunan abokin takararsa, ya iya yin kazafi da karya. dan siyasa shi ne wanda ya iya bakinsa; zai shara karya a yi masa kuwwa, ya yi rantsuwa ana yi masa tafi! Can a da ba haka abin yake ba. Wannan canjin da aka samu shi ya sa masu mutunci suke nisantar wannan muhimmin sha’ani da yake da alaka da rayuwar al’umma. Wani ma in ka ce masa “dan siyasa,” sai ya ga kamar ka zage shi. kauracewar mutanen kirki ga fage irin wannan shi ya haifar da ci bayan al’umma da tabarbarewar tsaro da lalacewar al’amura.
Siyasa a cikin Musulunci babi ne a ilimin Fikihu. Malamai sun tattauna ta a cikin babi na musamman. Daga bisani aka yi wallafe-wallafe wadanda suka mayar da siyasa ilimi mai zaman kansa. Daga cikin fitattun littattafan siyasa akwai As-Siyasa As-Shar’iyya na Shehun Musulunci Ibnu Taimiyya da Ad-duruk Al-Hukmiyya fi As-Siyasa As-Shar’iyya na Shaihin Malami Ibnu kayyim Al-Jauziyya. Kowanensu ya fi shekara dari bakwai da cikawa. A cikin wallafe-wallafen malaman jihadi na kasar nan akwai littafan siyasa, isali, Shehu Abdullahi dan Fodiyo ya wallafa Dhiya’us Siyasat da kuma Usul As-Siyasa.
Kalmar siyasa kalma ce ta Larabci wadda Bahaushe ya yi aronta, kuma a zahirinta tana nufin shugabanci ne, kamar yadda ya zo a cikin Hadisin Manzon Allah (SAW) cewa: “Banu Isra’ila tasusuhum al’anbiya.” Ma’ana: “Banu Isra’ila sun kasance Annabawa ke shugabantarsu.”
Kuma da wannan ma’anar ce mai Ishiriniya yake cewa: “Wasasa bizakal khalki linan wa shiddatan.” Yana nuni da siyasar Manzon Allah (SAW) ta shugabanci da duba maslaha wajen tsauri ko tausasawa.
Shugaba a Musulunci wakilin Manzon Allah (SAW) ne, don haka malamai suka duba tsarin shugabancin halifofi guda hudu suka ba su sunan tsarin Shugabancin Musulunci, kamar haka:
1. Halifancin Sayyidi Abubakar (RA) ya tabbata ne bisa ga nuni da wasicci daga Manzon Allah (SAW). Don haka, ya halatta shugaba ya nuna wani wanda ya cancanta a bayansa sai mutane su yi ma sa mubaya’a.
2. Shugabancin Sayyidi Umar (RA) ya tabbata ne bisa ga nadin da Sayyidi Abubakar (RA) ya yi masa a lokacin kusantowar ajalinsa bayan ya shawarci sahabbai. Saboda haka, yana inganta shugaba ya nada wa mutane wanda zai gaje shi amma ya shawarce su.
3. Shugabancin Sayyidi Usman (RA) ya tabbata ne bisa zaben ’yan Kwamitin Shura wanda Sayyidi Umar ya nada bayan da aka soke shi yana Sallah kuma ya ga ajali yana kusa. Don haka, malamai suka ce, ya inganta a kafa kwamitin dattawa masu hankali da basira da sanin abin da ya dace, su zabi shugaba guda daya daga cikinsu.
4. Shugabancin Sayyidi Ali (RA) ya wakana ne bayan da aka yi wa Sayyidi Usman (RA) juyin mulki aka yi masa kisan gilla. Sai al’ummar Musulmi mazaunan Madina a wancan lokaci suka cimma matsaya a kan tsayar da shi, kuma masu fada-a-ji daga cikinsu suka zabe shi, suka yi masa mubaya’a. Ke nan, ya halalta masu fada-a-ji su yanke shawarar wa zai zama shugaba ga al’umma.
Tsarin dimokuradiyya da ake bi a yau shi kuma ya dogara ne ga jefa kuri’a ta kowa da kowa. Mai ilimi da jahili, dan birni da dan kauye, mai basira da dolo…Haka ma Musulmi da kafiri duk matsayin kuri’arsu guda. Don haka, abin sa’a ne, idan masu son ci gaba da samar da maslaha suka fi yawa a cikin al’umma sai su zabi na kwarai ya shugabance su. Idan marasa kirki da mutanen banza suka fi yawa sai su zabi shashasha wanda zai jagoranci kasarsu gaba daya zuwa ga halaka.
Wannan tsari na dimokuradiyya kamar yadda muka sha fadi ba Musulunci ba ne. Domin Allah bai taba yarda a daidaita masoyanSa da makiyanSa ba. Bai amince a daidaita masu hankali da basira su zama daidai da dolaye ba. Allah Tabaraka wa Ta’ala yana cewa: “Shin wadanda suke da sani suna daidaita da wadanda ba su da sani? Abin sani ma’abuta hankali ne suke tunani.” Kuma Ya ce: “Rayayyu ba su daidaita da matattu, haka duhu bai daidaita da haske haka inuwa ba ta daidaita da rana….” Da sauran ayoyi irinsu da dama.
Duk wanda ma ya daidaita wadannan ya zama maras tunani.
Ya ku bayin Allah! Wannan tsari na dimokuraddyya da Allah Ya kawo zamaninsa yana da manufofi na zahiri da na boye. Dimokuradiyya a manufofinta na zahiri babu wani tsari da ya yi kama da Musulunci irinta. Suna cewa, shika-shikanta guda biyar ne:
1. Samar da nagartaccen shugabanci mai kula da hakkin jama’a.
2. Samar da zaman lafiya tsakanin mutane.
3. Samar da ’yanci da walwala a tsakanin daidaikun mutane.
4. Samar da adalci da ba kowa hakkinsa.
5. Hada kan jama’a su zama kasa daya al’umma daya don a samar da ci gaba.
Wadannan manufofin su ne na zahirinta, kuma a duk cikin wadannan ta yi tarayya da Musulunci. Domin duk suna cikin manyan manufofin da Musulunci yake tabbatarwa, amma a hakikani mu kalli siyasar kasar nan, sannan mu kalli siyasar duniya da ake ciki. Wadannan su ne abubuwan da siyasa ta tabbatar? A Najeriya tsakaninmu da Allah, mun fi zaman lafiya a zamanin dimokuradiyya ko kafin ta? Arzikin kasarmu, kafin zamanin dimokuradiyya aka fi wawashe shi ko a lokacinta? Yaushe ne muka fi samun hadin kai da ci gaba? Yaushe ne adalci da zaman lafiya suka fi wanzuwa?
Idan muka duba siyasar duniya, an kai dimokuradiyya a Iraki da Afghanistan da Mali da Somaliya da Masar da Libya da sauransu. Saboda Allah ci gaba suka samu ko ci baya?
Mu Kwana Nan