Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce yana nan da rai kuma yana cikin ƙoshin lafiya, duk da cewa wasu na masa fatan mutuwa.
Da yake magana a garin Osogbo yayin buɗe titin Old-Garage/Oke-Fia da Gwamna Ademola Adeleke ya sake ginawa, Obasanjo ya yi magana kan jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa ya mutu.
Ya ce, “Na ji jita-jitar cewa na mutu. Na gani a kafafen sada zumunta. Na gaggauta sanar da ’ya’yana da dangina cewa ba gaskiya ba ne kuma ina nan da raina. Waɗanda ke fatan na mutu, burinsu kenan, amma Allah Ya kare ni.”
Obasanjo, ya yaba wa Gwamna Adeleke bisa nasarorin da ya samu a Osun, kuma ya shawarce shi da ya ci gaba da gudanar da ayyuka masu kyau.
A nasa jawabin, Gwamna Adeleke ya tabbatar wa mutanen Jihar Osun, cewa gwamnatinsa za ta kammala dukkanin ayyukan da ake yi.
“Muna alfahari da gina hanyoyi sama da kilomita 120 a faɗin jihar nan,” in ji shi.
“Akwai gadoji biyu masu girma da suke gab da kammaluwa a Osogbo, kuma ana ci gaba da aiki a gadar Ile-Ife da kuma hanyar da aka ninka zuwa biyu a Ilesa.”
Ya ƙara da cewa, “Mun mayar da hankali kan kammala hanyar Iwo-Osogbo. Sannan, mun ƙara aikin gina hanyar Odoori-Adeeke a Iwo, wanda za a yi ta a matakai biyu.
“Matakin farko zai fara daga Post Office zuwa Fadar Oluwo, sannan mataki na biyu zai tashi daga Post Office zuwa mahaɗar Adeeke.”
Gwamnan, ya kuma jaddada cewa ba su ciyo bashi don yin waɗannan ayyukan ba.
“Ba mu karɓi wani bashi ba. Maimakon haka, mun toshe hanyar zurarewar kuɗin gwamnati, mun yi amfani da albarkatun cikin gida don rage kuɗin aiki,” in ji shi.