Bayan gaisuwa da girmamawa na rubuto maka wannan wasika ce, don in shaida maka tunanin al’ummar da ke wajen Kano kan abin da ke faruwa a Kano a tsakanin gwamnatinka da Masarautar Kano.
Da farko ina son ka sani Kano cibiya ce ta duk Hausa/Fulani da ke duniya. Cikin Hausa/Fulani goma na duniya biyar na da alaka da Kano ko ta auratayya, jini, asali ko kasuwanci ko wata hulda mai karfi.
Duk jihohin da ke da makwabtaka da Kano suna da alaka ta kut-da-kut da Kano ta daya daga abin da na fada a baya. misali a jihata Katsina. Yankin Sanatan Funtuwa mafi yawansu asalinsu Kanawa ne. Haka yake a yankin Sanata ta Daura, hatta Katsina a da tana karkashin Kano ne a zamanin mulkin Turawa.
A Katsina ta Tsakiya, kusan gida takwas cikin goma na da wata alaka da Kano, ta auratayya, jini, asali, ko kasuwanci ko wata hulda mai karfi. Ni marubucin nan tsatso ne daga jinin zuriyar Malam Muhammadu Bakatsine, da ’yar uwarsa Malama Jibado wadanda Katsinawa ne a asali amma da su aka yi jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo a Kano kuma sun taka rawa sosai kamar yadda tarihi ya tabbatar.
Wadannan dalilai suka sanya, duk abin da ya shafi Kano duk duniyar Hausa/Fulani kan amsa kuma yakan zama kamar amo ko’ina ka ji ya dauka a kan shiga damuwa kan lamarin sosai.
Yallabai, kana ba ni tausayi, don ana misalta ka da mutumin kirki, mai hakuri wanda miyagun mutane ke sarrafawa, don haka wani lokaci sai ka dauki matsayi bisa kuskure a lokacin da bai dace ba sai ka zama ba ka da goyon baya.
Rabuwarka da Kwankwaso, an dauka kai ne ka yi butulci don Kwankwaso ya kasance tare da kai a duk tsawon zamanku shekara takwas yana rike da mukamai ba ku da gwamnati a Kano. Ka yi ta daukar matsaya ta tafiyar da mulkin Kano wadda ta yi ta jawo maka karin bakin jini ga duk wani mataki da ka dauka, misali gina shaguna a filin Idi, da ginin gadar kasa a hanyar Zariya.
Hoton bidiyon da ake zargin kai ne, inda wani mutum na ba ka Dalolin Amurka a matsayin cin hanci da hana binciken don tabbatar da gaskiyar hotunan ya sa alamar tambaya da yawa a kanka. Fara daukar mataki a kan Masarautar Kano a cikin watan Ramadan ya daga wa duk Musulmi hankali ya kuma zama abin magana a wata Mai alfarma. Wannan ma ya jawo maka bakin jini ba dan kadan ba.
Duk wanda ke bin yadda lamura ke gudana a tsakanin gwamnatinka da masarautar, ya san ba ikhlasi a ciki sai dai wani aiki don huce takaici wanda wadansu ke zugawa ana yi.
Duk kuma abin da ba Allah ba ne asalinsa ba ya dorewa ko ba jima ko ba dade. Babban abin da ya kamata mutum ya fara kawowa a gabansa ga duk abin da zai fara shi ne tarihin da zai bari, wanda kuma zai rika bin sa da farautarsa ko bayan ransa.
Wace nasara aka samu da matsayar gwamnatin Kano ga masarauta? Rarraba kan al’umma daya mai karfin gaske,wadda ke magana da murya daya a da.
Kashe dimbin kudade don gaisuwa da wayar da kan mutane a kan matsayar da gwamnati ta dauka a kan masarautar, wanda duk mai bin shirye-shiryen rediyo da sauran kafofin sadarwa ya san ana kashe kudaden da suka kamata a saka su wani wajen da ya dace.
Kashe kudade don kawai a inganta sababbin masarautu, wadanda ya kamata a saka su a wasu ayyukan gina al’umma da ya fi dacewa. Dauke hankalin al’ummar Kano daga gaskiyar abin da ke ci musu tuwo a kwarya zuwa tattauna abin da ba zai amfani rayuwarsu kai-tsaye. Duk a wannan ba inda talaka zai amfana, sai dai Ranar Hawan Sallah Karama da Babba a yi a inda ya fito sai kuma Ranar Juma’a a je Sallah da kuma zaman fada.
Saboda kowa ya san cewa, a mulkin dimokuradiyya Kansila, Ciyaman, Dan Majalisar Jiha, na Tarayya da Sanata su ne kai- tsaye suke magana a kan al’ummarsu ba wani Sarki ko wata sabuwar masarauta ba.
Yallabai, wata rana za ka bar mulkin kuma bayan nan Allah ne Masanin wa zai amshe ka, kuma ya maye tsarinsa. A lokacin duk masu zuga ka za su guje maka. Wannan abin da ake wata rana kai za ta dawo maka da iyalinka kai ne za ai ta kawo tarihi ana danganta shi da kai, a lokacin kowa zai juya maka baya yana fadin cewa kai ne ka sanya shi.
Yana da kyau a saka hangen nesa a kuma sanya kula komai mutum zai gabatar ya tuna cewa wata rana yaya abin zai dawo masa kuma ya zama masa tuhuma, mai ba da shaida kuma alkalin kansa da kansa.
A kan bincike na masarauta, a wannan zamanin da muke ciki wane ne za a bincika ya tsallake ba a same shi da laifi ba? Wata rana za ka bar mulkin kana fata a yi maka binciken kwakwaf?
Bincike don bata suna bai hana abin da Allah Ya tsara bawa zai yi nasara a kansu na rayuwa, misali zamanin Abacha na Shugaban Kasa, ya sanya an yi wa tsohon Gwamnan Kano Kabiru Gaya binciken terere wanda aka rika yada abin a gidan rediyo kai-tsaye da ba da labarin a sauran kafofin watsa labarai yanzu Kabiru Gaya Sanata ne, daga Jihar Kano a karo na uku. Ina rokon a sa hankali, lura da hangen nesa don gaba don wata rana ko don zuriya da iyali da sauran al’umma.
Danjuma Katsina
Mawallafi ne kuma dan jarida
Ana iya samunsa a: [email protected] 08035904408