✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasan Roma da Barcelona: Wani ya rataye kansa a Ilori

Wani mutum dan kimanin shekara 25 ya kashe kansa ta hanyar sargafe wuyansa da igiya a garin Ilori da ke Jihar Kwara. Kamar yadda wani…

Wani mutum dan kimanin shekara 25 ya kashe kansa ta hanyar sargafe wuyansa da igiya a garin Ilori da ke Jihar Kwara.

Kamar yadda wani rahoton ya nuna, mutumin ya kashe kansa ne ta hanyar rataye kansa da wata igiya da ya daura a saman dakinsa ba tare da sanin kowa ba.

Kamar yadda rahoton ya nuna, mutumin ya kashe kansa ne saboda takaicin ganin yadda ya rasa babur dinsa da yake yin acaba a cacar kwallon kafa da suka yi da wani a gidan kallon kwallon kafa a ranar da aka yi wasa a tsakanin kulob din AS Roma na Italiya da kulob din FC Barcelona  wasa karo na biyu a gasar zakarun kulob na Turai da ya gudana a ranar Talatar makon jiya. 

An ce mutumin, wanda dan ga-ni-kashe-nin FC Barcelona na Sifen ne, yana yin acaba ne da hakan ta sa ya yi amfani da babur din wajen shiga cacar kwallon.

 Mutumin yana da tabbacin  Barcelona ce za ta samu nasara a wasan, ganin yadda a wasan farko ta lallasa AS Roma ne da ci 4-1 amma abin mamaki sai Roma ta samu nasara a kan Barcelona da ci 3-0, da hakan ya sa ta fiyar da Barcelona.  Jim kadan bayan an tashi wasan ne sai mutumin ya rasa babur dinsa a harkar cacar da hakan ta sa ya harzuka ya koma gida cikin fushi.

A washegari ne da ba a ji motsinsa ba, sai aka balle kofar dakinsa sannan aka ga halin da yake ciki.

Al’amarin ya faru ne a garin Oko-Erin da ke garin Ilorin.

Wani wanda al’amarin ya faru a kan idonsa ya shaidawa manema labarai cewa mutumin dan kabilar Ibo ne, kuma ’yan uwansa sun kadu matuka game da faruwar wannan lamari.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta Jihar Kwara Mista Ajayi Okasanni ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, sai dai ya ce akwai yiwuwar marigayin ya kashe kansa ne saboda basussukan da suka yi masa katutu.  Ya ce a binciken da suka yi, sun gano ana bin marigayin bashi a wurare da dama da ya kasa biya, da hakan ta sa ya yanke shawarar kashe kansa.

Ya ce rundunarsa za ta ci gaba da yin bincike don gano dalilin da ya sa marigayin ya rataye kansa.  Ya hori jama’a da su rika kai zuciya nesa a duk lokacin da wani abu ya dame su a rayuwa don gudun fadawa cikin irin wannan al’amari.