Daya daga cikin mutanen da aka cinna wa wuta a lokacin da suke sallah a wani masallaci a Jihar Kano ya rasu a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad.
Mataimakin Shugaban ’Yan Sandan Mai Kula da Shiyya ta Daya, AIG Umar Mamman Sanda ne ya bayyana hakan yayin da shi da kwamishinan ’yan sandan jihar Kano da Daraktan Hukumar DSS da sauran shugabannin hukumomin tsaro suka ziyarci wadanda suka kone a masallacin da ke kwance a asibitin.
“Daga cikin mutane 24 da aka kawo asibiti, daya ya rasu, abin takaici ne matuka,” in ji AIG Sanda.
Ya kara da cewa rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama matashin da ake zargi da cinna wa mutanen wuta a masallacin da ke kauyen Larabar Abasawa a Karamar Hukumar Gezawa.
- An kama matashin da ya cinna wa mutane wuta a masallaci a Kano
- Matashi ya cinna wa mutane wuta suna sallar Asuba a masallaci a Kano
Ya kara da cewa, “A halin yanzu yana tare a hannunmu kuma yana bayar da bayanai masu amfani.
“Wanda ake zargin ya yi amfani da wani abin fashewa da aka kera a cikin gida domin aikata wannan mummunar ta’asa.”
“Abin da ya faru ba shi da wata alaka da ta’addanci ko wata kungiya, kawai rigima ce ta rabon gado da ta ki ci ta ki cinyewa.
“An ce wanda ake zargin bai gamsu da rabon da aka yi ba ne ya yi wannan aikin, kuma hakan a wurinsa martani ne kan abin da yake zargin an yi masa na ba daidai ba,” in ji shi.
AIG Umar ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu domin kuwa hukumomin tsaro a jihar za su yi abin da ya dace.