✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasan kwallon kafa na ’yan kasa da shekara 17 a Yamai: Najeriya ta lallasa Nijar da ci 2-0

An fara gasar cin kofin wasan kwallon kafa na ’yan kasa da shekaru 17 (U-17)a ranar Lahadin da ta wuce a filin wasa na Seini…

An fara gasar cin kofin wasan kwallon kafa na ’yan kasa da shekaru 17 (U-17)a ranar Lahadin da ta wuce a filin wasa na Seini Kounthe dake cikin garin Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar. Wasan wanda aka fara karawa a tsakanin Najeriya mai rike da kofin da kuma Nijar mai masaukin baki,Najeriya ce ta lallasa Nijar da ci biyu da nema.

kasashe takwas ne suka fafatawa a gasar inda aka kasa su gida biyu watau kowacce shiyya tana dauke da kasashe hudu. . Rukunin farko ya hada da Najeriya da Nijar da Guinea da kuma Zambia. Sai rukuni na biyu da ya hada da Afrika ta Kudu da Ibory Coast da Kamaru da Mali. 
A lokacin bude gasar, Ministan wasanni na Jamhuriyar Nijar Malam Abdulkarim danmalam ya nuna farin cikinsa akan damar da kasarsa ta samu na daukar nauyin bakuncin wasan ta bana. Ministan wanda ya halarci filin wasan tare da wasu mukarraban gwamnatin Nijar ya ja hankalin ‘yan wasan akan muhimmancin wasanni tare da fatan yadda aka fara wasan lafiya za a kuma kare shi lafiya.
Najeriya dai ta sake buga wasanta na biyu ne a shekaranjiya Laraba da kasar Guinea yayin da za ta yi wasa na uku a gobe Asabar idan Allah ya kaimu da kasar Zambiya.
kasashe hudun da suka kai matakin kusa da na karshe (semi-fainal) ne za su haye gasar cin kofin duniya na matasa na ’yan kasa da shekara 17 da zai gudana a watan Nuwamban wannan shekara.