Wasanin dambe ko kokawa na daya daga cikin wasannin gargajiya da jama’a da dama suke nuna sha’awarsu a kai. Za a ga ana fafatawa a tsakanin matasa majiya karfi don sa al’umma nishadi walau a wajen bukukuwan Sallah ko kuma a hada gasa a saka kyaututtuka ga duk wanda ya samu nasara. Ganin muhimmancin wasannin ya sa wakilanmu suka jiyo ra’ayoyin mutane a kan wanne ne ya fi nishadantar da su a tsakanin dambe da kokawa?
Kokawa ta fi dambe saka nishadi ga mai kallo – Muhammad Sani Isah (Sani King) Layin Allasure, Kano
Daga Faruk Tahir Maigari
Idan aka dubi kokawa ta fi saka nishadi domin za ka ga dan karamin mutum ya wulwula kato sama ya fyada shi da kasa.Ana amfani da tsabar hikima ce ba wai karfi ba, girman mutum ba ya sawa ka ce shi zai yi nasara dole sai an fafata ake sanin jarumi.
Kokawa ta fi sa nishadi – Ali Dan Baba
Daga Musa Kutama, Kalaba
Magana ta gaskiya ni dai gara wasan kokawa ya fi nishadantar da ni ya fi kuma burge ni domin saboda za a yi taga-taga a tsakanin ’yan wasa. Shi kuwa dambe duk inda ka samu naushewa za ka yi. Kokawa kuwa wata dabara ce da ake hada jiki har a yi kaye.
Dambe ya fi kokawa sanya nishadi – Ibrahim Adamu (scorer) Mai aski, Tudun Maliki, Kano
Daga Faruk Tahir Maigari
Ni a ra’ayina dambe ya fi kokawa burgewa da sa nishadi a zukata. Duk wani jarumi zai yarda da ni cewa dambe ya fi nuna jarumta da bajinta domin idan ka yi dubi da yadda ake amfani da karfi da hikima a lokaci guda, za ka ga a cikin lokaci kankane za a yi shi a gama ba tare da kosawar mai kallo ba. Sabanin kokawa da za ka ga wani lokacin an dauki kusan sa’a guda ana fafatawa.
Dambe ya fi kokawa – Uba Sale Mainama Bakin Kasuwar Bolori
Daga Muhammad Aminu Ahmad
Ni a ra’ayina dambe ya fi kokawa, ya fi sa ni cikin nishadi. Domin nakan dauki nauyin ’yan dambe tun daga Legas a zo nan Maiduguri a yi wasan dambe. Mu sa kyaututtuka ga duk dan damben da ya yi nasara kai har mota na taba sa wa don sha’awata ga wasan dambe. Gaskiya babu ma hadi a tsakanin wasan dambe da kokawa, dambe ya fi sa nishadi.
Dambe ya fi nishadi – Muhammad Kabiru
Daga Musa kutama, kalaba
Ni gaskiya dambe ya fi nishadantar da ni ya kuma fi burge ni. Saboda shi ne wasan da duk wanda ya je ya kalla sai ya dawo da nishadi a ransa. Kuma wasa ne na masu karfi dalilin da ya sa ke nan ya fi nishadantar da ni ya fi burge ni.
Gaskiya dambe ya fi –Muhammad Sani Bakin Kasuwar Bolori
Daga Muhammad Aminu Ahmad
Alhamdulillahi gaskiya dambe ya fi nishadantar da ni, saboda tun ina karami nake sha’awar wasan dambe nake gani ake yi a gabana. Kullum idan ina kallon wasan dambe yana kara min jin dadi. Kuma na fi sha’awarsa a kan wasan kokawa, don muhimmancinsa har Makkah ake kai mutum a kan wasan dambe don akwai albarka a cikinsa.