✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wanzaman gargajiya za su yi wa marayu 100 kaciya kyauta a Yobe

Kungiyar Masu Maganin Gargajiya da Wanzanci ta Kasa reshen Fataskum a Jihar Yobe, ta shirya yi wa yara marayu guda 100 kaciya kyauta. Za a…

Kungiyar Masu Maganin Gargajiya da Wanzanci ta Kasa reshen Fataskum a Jihar Yobe, ta shirya yi wa yara marayu guda 100 kaciya kyauta.

Za a yi aikin ne a ranar 23 ga watan Janairun shekarar 2022, a fadar Sarkin Fika da ke garin Fataskum a Jihar.

Shugaban kungiyar wanda har ila yau shi ne Sarkin Askar Fataskum, Dokta Aminu Abdullahi, ne ya bayyana hakan ga wakilnmu, inda ya ce kungiyarsu ta damu da halin da yara marayun ke ciki.

“Kaciya an fi yin ta a lokacin sanyi, amma mu wacce muke yi ta musamman ce saboda muna la’akari da yanayi na kiwon lafiya da sauran matakan da ake bi, domin Allah ya hore mana baiwa da idan muka yi wa yaro zai sa wandonsa nan take,” inji Sarkin Asakar.

Ya kuma ce tuni suka zakulo wasu marayun da ba su da masu daukar nauyinsu don yi musu kaciyar kyauta sannan kuma za a samar musu da tufafi a lokacin.

Sarkin Askar na Fataskum ya yi jinjina ta musamman isa ga irin hadin kai da goyon baya da suke samu daga Sarakunan gargajiya.

Daga nan sai ya ce suna gayyatar dukkan abokan sana’arsu wanzamai daga jihohin arewa dan shaida aikin.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da kungiyar take irin wannan aikin, domin ko a ranar 13 ga watan Janairun 2020 kungiyar ta yi wa marayu sama da 200 irin wannan hidima a fadar mai martaba Sarkin na Fika.