✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wani soja ya harbe kwamandansa a Borno

Ya harbi hafsan sau takwas ta baya daga kusa-kasa a yayin da suke aiki tare

Wani kurtun soja ya hallaka kwamandansa bayan ya yi masa ruwan harsasai a yankin Bama na Jihar Borno.

Sojan ya harbe Laftanar Babakaka Ngirgi sau takwas, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar hafsan a ranar Laraba.

Majiyarmu ta soji ta ce kurtun wanda yanzu yake tsare ya dade yana kullatar hafsan wanda suke aiki tare a Bataliyar Tankoki ta 202 a Karamar Hukumar Bama ta Jihar Borno.

Ta ce kurtun ya bude wa mamacin wuta ne ta baya kuma a kusa da shi, inda nan take ya rasu.

A ranar Alhamis za a yi jana’izar Laftanar Babakaka Ngorgi a barikin sojan kasa na Maimalari da ke Maiduguri.

Majiyar ta ce a ‘yan shekarun an samu irin wannan matsalar tsakanin sojoji rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram a Gwoza, Chibok, Bama da kuma Mallam Fantori.

Mamacin ya kammala kwalejin kananan hafsoshi ta NDA ne a 2016, sannan ya yi aure watan Disamban 2019.