✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani mutum ya shiga hannu kan zargin sace dan jarida a Ogun

Ana zargin mutumin da sace dan jarida a jihar.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta kama wani mutum mai shekara 41 bisa zarginsa da garkuwa da wani dan jarida a jihar.

A ranar 24 ga watan Maris ne rundunar ‘yan sandan ta kama shi a matsayin daya daga cikin wadanda ake zargi sun yi garkuwa da dan jaridar, Olusegun Oduneye, a unguwar Mobalufon da ke Ijebu-Ode a ranar 9 ga Maris, 2023.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan “binciken fasaha da leken asiri” da rundunar ‘yan sandan da SP Taiwo Opadiran ke jagoranta, suka gano maboyar da wanda ake zargin.

Oyeyemi, ya ce ana zargin mutumin da ya shiga hannu ya tsare dan jaridar da suka sace a wani waje a daji, yayin da abokansa ke jiran ‘yan uwa da abokan arzikin dan jaridar su kawo kudin fansa.

Ya kara da cewa wanda ake zargin ya gudu bayan ya gano cewa sauran abokan sun samu rauni a yayin artabu da ‘yan sanda.

Oyeyemi ya bayyana cewa, “Mun yi sa’a mun gano maboyarsa a yankin Ijebu-ode inda a nan aka kama shi,” cewar Oyeyemi.

Ya kara da cewar an samu bindiga da kuma harsashi a hannun wanda ake zargin.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Frank Mba, ya umarci rundunar da ta kara kaimi wajen cafke sauran abokan aikin nasa.