Wani mutum ya yanke jiki ya mutu nan take yayin da yake tsaka da bin layin cirar kudi a wani banki a Karamar Hukumar Ika ta Kudu a Jihar Delta.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mutumin ya shafe sa’o’i yana bin layin cirar kudi a na’urar ATM yayin da karar kwana ta cim masa.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 41 a Bakori
- Za mu dage mulkin Najeriya ya koma hannun mutanen Kudu a Zaben 2023 —El-Rufai
Jami’in Hulda da Al’umma na Rundunar ’Yan sandan Jihar Delta, DSP Bright Edafe ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar DSP Edafe, “mutumin wanda ya dade a kan layi domin cirar kudi ya zo ne domin karbar katinsa na ATM.”
A halin yanzu dai jama’ar kasar na ci gaba da gunaguni dangane da karancin sabbin takardun Naira da aka sauyawa fasali, la’akari da yadda wa’adin karbar tsohuwar Nairar ya karato.
A ranar Lahadin da ta gabata ce Babban Bankin Najeriya CBN ya tsawaita wa’adin amfani da tsohuwar naira da kwanaki goma.
A cewar Babban Bankin, wa’adin karbar tsohuwar Nairar zai cika a ranar 10 ga watan Fabrairu, wanda kuma Gwamnan na CBN, Godwin Emefiele ya ce babu gudu babu ja da baya.
Aminiya ta ruwaito yadda zanga-zanga ta barke a jihohin Oyo da Delta dangane da yadda jama’a ke ci gaba tagayyara saboda karancin sabbin takardun kudaden a hannun jama’a.