Wani mutum dan kasar Tanzaniya mai suna Patrick Kimaro, ya girgiza jama’ar kauyensu bayan ya gina wa kansa kabari don rage wa iyalansa nauyin kudaden da za su kashe bayan mutuwarsa.
Patrick Kimaro, mai shekaru 59, ya ce jama’ar yankin nasu na masa wani kallo na wanda ya samu tabin hankali.
“A matsayina na dan fari, na sha wahala wajen binne iyayena lokacin da suka mutu tsakanin watanni shida… don haka na yanke shawarar ba zan bar wa ‘ya’yana irin wannan wahalar ba,” a cewarsa.
Shugabannin gargajiya daga kabilar Mista Kimaro da ke yankin Kilimanjaro a kasar, sun ce hukuncin nasa ya saba da dokokin al’adun yankin.
Mutumin wanda ke aiki a matsayin dan sanda, ya shaida wa manema labarai cewar, ya fara gina kabarinsa ne a watan Janairu domin ya rage wa iyalinsa kudaden jana’iza idan ya mutu.
Mista Kimaro yana shirin ware wasu kudade don hada akwatin nasa kuma ya yi imanin cewa iyalansa za su iya tara kudade don wasu abubuwan da suka shafi mutuwarsa.
Kazalika, ya kuduri niyyar biya wa kabarin nasa inshora ko da wani abu zai taso ya gaza karasa cimma kudurin nasa.
Kimaro ya kashe zunzurutun kudi har kimamin Dala $3,000 wajen haka tare da kawata kabarin nasa.
Jami’in tsaron gidan Mista Kimaro ya ce wasu makwabta sun kaurace wa kai ziyara gidan tun bayan fara hakar kabarin.
Wasu daga cikin dangin Mista Kimaro sun goyi bayansa inda suka taimaka masa wajen kammala hakar kabarin nasa.