✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wani mutum ya fille kan abokinsa

An fille kan wani manomi mai suna Adoja Tanaku bayan wata rigima da ta barke tsakaninsa da abokinsa a Ibadan, Jihar Oyo. Mutumin wanda shi…

An fille kan wani manomi mai suna Adoja Tanaku bayan wata rigima da ta barke tsakaninsa da abokinsa a Ibadan, Jihar Oyo.

Mutumin wanda shi da abokin nasa da ya kashe ’yan asalin Jamhuriyar Benin ne, ya tafka aika-aikar ne a unguwar Bakatari da ke garin Ibadan.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Oyo, Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da aukuwar lamarin da cewa an kai gawar mamacin mucuwari.

Ya ce rundunar na tsare da manomin da ake zargin ana bincike a ofishin ’Yan Sanda na Eleyele.

A wani labari kuma, ’yan fashi sun kashe dan uwan ​​kwamishinar Ayyuka na Musamman, Funmilayo Orisadeyi a garin na Ibadan.

’Yan fashin sun harbi Isaac Orisadeyi, mai shekara 45 ne a kan titin Nihort-Idi-isin ranar Talata da dare.

Majiyarmu ta ce kwamishinar ta ce asibitoci biyu sun ki karbar shi kafin daga baya rai ya yi halinsa.

Abin ya faru ne a lokacin da Isaac ke kan babur a kan hanyarsa ta komawa daga aiki da misalin karfe 8 na dare lokacin da lamarin ya faru.

Masu kwacen babur din sun bude wuta ne bayan dan acabar da ya dauki Isaccya bijire musu a lokacin suka yi kokarin kwace babur din.