✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wani mutum ya cinna wa gidansa wuta da iyalansa a ciki

Ya cinna wa gidansa wuta a sakamakon sa'insa da ta shiga tsakaninsa da matarsa.

Wani mutum mazaunin Unguwar Eyenkorin a birnin Ilorin na Jihar Kwara, ya cinna wa gidansa wuta a sakamakon rashin jituwa da ya shiga tsakaninsa da matarsa.

Jami’in hulda da al’umma na hukumar kwana-kwana ta jihar, Hassan Adekunle da ya tabbatar da hakan, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3.00 na ranar Lahadi.

Hassan Adekunle ya ce wani mutum mai suna Mista Kola ne ya yi gaggawar kiran hukumar kashe gobara kan lamarin.

Da yake zantawa da wakilinmu ta wayar tarho, Adekunle ya ce hukumar ta yi nasarar kashe gobarar tare da hana ta tashi zuwa wasu gine-gine da ke makwabtaka da gidan.

“Abin da muka samu shi ne, mutum da ya kira mu ba zai iya tuna sunan magidancin ba a yanzu.

“Sai dai ya sanar mana cewa rashin fahimtar juna da suka samu da matarsa kimanin shekaru biyu da suka gabata ce ta sa ya koma wani gidan da zama ya bar matar da ’ya’yansa ciki.

“Duk kokarin da aka yi na sasanta lamarin bai haifar da da mai ido ba, sannan kuma yunkurin da aka yi na shawo kansa ya bar matar da ’ya’yansa su zauna a gidan tunda yana da wani gidan shi ma ya ci tura.

“A cewar rahoton, kwatsam sai ga mutumin ya bayyana a ranar Lahadi, ya kuma watsa man fetur a dakunan kwana uku, ya cinna wa gidan wuta alhali matar da yaransa na ciki.”

Adekunle ya ce ba don daukin da mazauna yankin da kuma mika rahoton da aka yi ga hukumar dangane da faruwar lamarin, da tuni yanzu labari ya sha bamban.