Wani magidanci mai matsakaicin shekaru, mai suna Ali Harazimi ya rataye kansa.
Magidancin mazaunin unguwar Ja’en Layin Makera a cikin birnin Kano, ya rataye kansa ne a jikin bishiya, a unguwar Samegu da ke kan hanyar zuwa Madobi daga Kano.
Binciken Aminiya ya gano cewa mutumin ya bar gidansa ne da dare ranar Lahadi inda ya je ya rataye kansa a bayan gari a Unguwar Samegu, inda washegari mazauna unguwar suka wayi gari suka ga gawarsa a rataye.
Yayan marigayin Alhaji Yakubu Hamisu, ya shaida wa Aminiya cewa ya yi ta jiran Ali Harazumi ya zo su yi sahur a gidansa kasancewar a yanzu ba ya da mace. Ya ce, “Na jira shi na ga bai zo ba, sai na buga wayarsa don na kira shi, amma sai na ji bai dauka ba, sai na zaci ko barci ne ya dauke shi, kamar yadda hakan ya taba faruwa a farkon azumin nan.”
Ya ce da gari ya waye ya ga bai ga dan uwan nasa ya zo wurinsa kamar yadda ya saba ba, sai ya fara tunanin ko ba lafiya ba. Ya kara da cewa suna cikin cigiyarsa ne, kwatsam sai ya ji an bugo masa waya daga ofishin ’yan sanda, aka sanar da shi abin da ya faru, kuma aka bukaci ya je wurin ajiyar gawa na asibiti, domin ya sa hannu a ba shi gawar dan uwansa.
Yayan marigayin ya ce bai san dan uwan nasa da tabin hankali ba, sai dai ya san cewa marigayin ya rasa sana’arsa ta acaba, sakamakon hana yin sana’ar da aka yi a birnin Kano da kewaye. Haka nan ya ce dan uwan nasa ya jima da rabuwa da matansa, “Domin a baya ya auri mata daban-daban har shida, yana saki yana aurar wasu, daga baya ya rabu da matarsa ta karshe,” inji shi.
Ya ce idan da wani abu da yake damun Ali Harazumi, bai wuce na takaicin rashin aure ba, domin ya ce duk da rashin sana’arsa da ya yi, bai rasa ci ko sha ba, domin dan uwan nasa yana taimaka masa. Haka ya ce marigayin yana da gidan kansa, ba haya yake yi ba, don haka damuwarsa kadan ce. Sai dai kuma ya ce a kwanakin nan ya ji mahaifiyarsu tana cewa za ta kai Ali Harazumi wajen malamai, domin su yi masa taimako na maganin aljannu, saboda lura da ta yi na sauyi a halayyarsa.
Alhaji Yakubu ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun je wurin da lamarin ya faru suka yi bincike, sannan sun yi masa tambayoyi, tare da bayyana masa za su ci gaba da bincike a kan lamarin. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano Mataimakin Sufurtandan ’Yan sanda Magaji Musa Majiya ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin inda ya ce marigayin ya bar rubutacciyar takarda mai dauke da sunansa da lambar wayar yayansa, wacce ta taimaka aka gano dan uwan nasa.
Wani magidanci ya rataye kansa a Kano
Wani magidanci mai matsakaicin shekaru, mai suna Ali Harazimi ya rataye kansa.Magidancin mazaunin unguwar Ja’en Layin Makera a cikin birnin Kano, ya rataye kansa ne…
