✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wani kulob zai mayar wa magoya bayansa kudin tikitin shiga wasa

Wani kulob da ke buga wasa a rukunin ’yan dagaji (amateur) a Meziko mai suna Irapuato ya yanke shawarar mayar wa magoya bayansa kudin tikitin…

Wani kulob da ke buga wasa a rukunin ’yan dagaji (amateur) a Meziko mai suna Irapuato ya yanke shawarar mayar wa magoya bayansa kudin tikitin shiga filin wasansu don kallon yadda wasansu ya kaya a makon jiya, bayan kulob din ya sha kashi a karo na biyu a jere.
Kamar yadda kulob din ya sanar a ranar Talatar da ta wuce a kafar sadarwarsa ta Twitter, ya ce ya yanke shawarar mayar wa  magoya bayansa kudin tikitin da suka kashe ne bayan ya sake shan kashi a karo na biyu a jere, inda ya bukaci magoya bayan su gabatar da tikitinsu don a mayar musu da kudinsu ba tare da bata lokaci ba.
Kimanin magoya baya dubu 8 ne ake sa ran kulob din zai mayar musu da kudin tikitin da suka kashe.