Wani dan Uganda mai suna Fahad Musana kuma dan ga-ni-kashenin kulob din Chelsea na Ingila ya sheka barzahu jim kadan bayan dan kwallon kulob din Manchester City Frank Lampard ya rama cin da Chelsea ta yi masu a gasar rukunin firimiya na Ingila a ranar Lahadin da ta wuce.
Mutuwar dan kwallon, mai kimanin shekara 24 ta girgiza daukacin al’ummar yankin jami’an kulob din da yake yi wa kwallo mai suna Simba FC musamman ganin yana daga cikin wadanda suka buga wa kulob din wasa a ranar Asabar inda kulob din nasu ya doke na Entebbe FC a gasar rukunin Uguanda da ci daya mai ban haushi. A washegari ne watau a ranar Lahadi marigayin ya gamu da ajalinsa a lokacin da yake kallon wasa a tsakanin kulob din Chelsea da na City a wani gidan kallon kwallo a unguwarsu.
Kocin Simba mai suna Fred Kajoba ya tabbatar da wannan labari na mutuwar Fahad. Ya ce marigayin ya halarci atisaye da kulob din Simba a ranar Lahadi da safe kamar yadda suka saba amma da maraicen ranar ne suka samu labarin mutuwarsa. “Mun yi atisaye da marigayin lafiya kuma a lokacin bai nuna wata alama ta rashin lafiya ba amma kwatsam sai muka samu labarin ya rasu da maraice bayan an gama wasan Chelsea da na Manchester City a Ingila”.
Rahoton da muka samu ya tabbatar dan kwallon ya kamu da matsananciyar rashin lafiya ce da ake kayuata zaton bugun zuciya ce a lokacin da yake kallon gasar rukunin Ingila a wani gidan kallon kwallo.
An shaidi marigayin a matsayin mai matukar kaunar kulob din Chelsea, kuma yana cikin annashuwa da murna a lokacin da kulob din Chelsea ya zura kwallo a ragar City amma jim kadan da Frank Lampard ya rama cin da Chelsea ta yi wa City ne sai aka ga ya zube kasa yana kakkarwa inda aka garzaya da shi asibiti kafin wani lokaci ne ya ce ga garinku.
Wani kulob zai mayar wa magoya 1 bayansa kudin tikitin shiga wasa
Wani dan Uganda mai suna Fahad Musana kuma dan ga-ni-kashenin kulob din Chelsea na Ingila ya sheka barzahu jim kadan bayan dan kwallon kulob din…