✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wani dan shekara 62 ya rataye kansa a Ondo

Mutumin ya rataye kansa kafin iyalinsa su dawo daga gona.

An tsinci gawar wani mai shekara 62 a duniya mai suna Moshood Lasisi a dakinsa da ke Unguwar Ayede Ogbese a Karamar Hukumar Akure ta Arewa a Jihar Ondo.

Aminiya ta ruwaito cewar, Lasisi ya rataye kansa kafin matarsa ​​da yaransa su dawo daga gona kwanaki biyu da suka gabata.

  1. Kisan Jibiya: Ku dauki makami ku kare kanku —Masari
  2. Matsalar tsaro: Matasa sun yi zanga-zangar lumana a ’Yantumaki

Bayanai sun ce bayan dawowar iyalansa ne matarsa, Lady Evangelist Victoria Lasisi ta rika kwankwasa kofa ba tare da jin motsinsa ba.

Daga bisani sai ta leke ta taga inda ta yi ido hudu da gawarsa rataye tana reto a jikin wata igiya da ya daure kansa.

Ganin haka ke da wuya kwalla ihu, lamarin da ya janyo hankalin makwabta suka fito babu shiri domin kawo dauki.

Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN a yankin, Fasto Oyedeji Aladenika, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma mamaki kan dalilin da ya sa mutumin ya kashe kansa.

Fasto ya ce duk da cewa mutumin na da matsalar kafa, matarsa ​​da yaransa suna kula da shi.

Kokarin jin ta bakin kakakin ‘yan sandan Ondo, Odunlami Funmilayo ya ci tura zuwa lokacin hada wannan rahoto.