Masallacin Annabi (SAW), Madina
Fassarar Salihu Makera
Godiya ta tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabin mai girma da alayensa da sahabbansa.
Bayan haka ya ku ’yan uwa Musulmi! Yin magana a game da manyan malamai ba abu ne mai sauki ba, kuma ko ka yi kokarin tsakuro wani abu daga rayuwar daya daga cikinsu da wuya ka yin hakan. Domin kana iya barin wasu muhimman abubuwa masu ban sha’awa da suka shafi rayuwarsa.
Rayuwar manyan magabatan malamai babbar abar misali ce da za ta karfafa matasanmu ta yadda za ta hana su koyi da miyagun mutane wadanda ba su da wani abin kirki da za su nuna a wannan rayuwa ko wani abin kirki ga tarihin rayuwar dan Adam.
Maganarmu a kan malamai ba ta nufin karkata ga dayansu ba ne, domin kowane mutum ana iya karbar maganarsa ko a yi watsi da ita, face maganganun Shugabanmu Annabi Muhammad (SAW).
Wanda za mu magana a kansa a yau shi ne babban Imam wanda ya taso a birnin Madina, wanda ambaton sunansa yake faranta rai, wanda iliminsa ya cika bayan kasa. Ya koyar da mutane a cikin Masallacin Annabi (SAW), inda ya yi fice sosai ta yadda in aka ce: “Malamin Madina” ko “Imamu Darul Hijira” ba wani ake nufi ba face shi.
Malik bin Anas (RA), an haife shi ne a birnin Madina, ya tashi a can a matsayin mai so da neman ilimi duk da halin da talaucin da yake ciki. Mahaifiyarsa ta yi masa kyakkyawar tarbiyya inda ta umarce shi da cewa” “Ka je wurin Rabi’ata ka koyi kyawawan dabi’unsa kafin ka nemi ilimi.”
Wannan mace ta san nauyin da ke kanta a rayuwa da kuma wajibcin da ke kanta na ilimantarwa da tarbiyyantar da matashin danta. Ta san cewa kyawawan dabi’u su ne kyawawan abokan tafiyar ilimi, kuma ilimi ba ya da amfani idan babu kyawawan dabi’u. Wannan uwa takan gina mutum kuma ta haka takan gina kasa.
Rawar da uwa take takawa ba ta tsaya a kan rainon gangar jiki kadai da kare shi daga cututtuka ba. A’a, tana da babban aikin da ake so ta cimmawa. Aikin ya hada da karfafa imani da gina kakkarfar mutumtaka da bunkasa tunani da ilimi da kuma karfafa wa ’ya’ya su zamo masu martaba. Dukan wadannan ba za a same su ba face tun farko an fifita cusa musu kyawawan ayyuka a zukata a yayin yi musu tabiyya fiye da damuwa da abin duniya.
Wannan shi ne hakikanin abin da ya faru a rayuwar Imam Malik, kuma wannan ne ya sanya shi kansa ya zama wata makaranta ta kyawawan dabi’u da daliban ilimi suke koyi da shi, kuma daukacin al’umma take cin gajiyarsa.
Imam Malik ya taba fada wa wani matashin Bakuraishe cewa: “Ya kai dan ummata! Ka koyi kyawawan dabi’u kafin ka koyi ilimi.”
Yahya bin Yahya At-Tamimi ya ce: “Na zauna tare da Imam Malik na tsawon shekara daya bayan na kammala karatuna a wurinsa domin in koyi kyawawan dabi’u da kyawawan halaye daga gare shi. Kuma halayensa irin na sahabban Annabi (SAW) ne da wadanda suka biyo bayansu.”
’Yan uwa a cikin imani! Hanyoyin koyar da ilimi na zamani a wasu lokuta sukan nuna cewa sun yi nesa da duk wani abu da ya shafi kyakkyawan hali, wanda hakan ya sanya ilimi ya rasa kimarsa da tasirinsa ga mai shi. Idan aka raba ilimi da kyawawan halaye – to duk yawan ilimin da za a samu – za a ga babban tasgaro kan tasirinsa ga halayen mutanen ko tsabtace ayyukansu. Don haka babu alheri a cikin ilimin da ba za a samu kyawawan halaye ba.
Haifar da gibi a tsakanin ilimi da kyawawan halaye yana haifar da miyagun dabi’u kamar suka da bata malamai da zafafa magana a kansu da mugub hali da wulakanta iyaye da makauniyar biyayya ga kafirai a al’amuran da suka shafi sutura da ta’adda a kan malaman makaranta da masana ilimi ya alla ta jikinsu ko fadin miyagun maganganu a kansu.
Madina birnin Annabi (SAW) ya taka gagarumar rawa a rayuwar Imam Malik, saboda cike yake da manyan malaman Musulunci. Makaranta ta farko a tarihin Musulunci ita ce Masallacin Annabi (SAW), kuma a kowane lokaci akwai ajujuwan da ake koyar da ’ya’yan Musulmi kyakkyawan ilimi da ke ba su damar kasancewa masu ilimin addini kuma masu kyawawan halaye da dabi’u.
Ya ’yan uwa Musulmi! Abu ne sananne cewa abin da mummunan muhalli (mugun abokin zama) abin da yake yi shi ne lalatawa ba ginawa ba. Idan ba haka ba, mene ne amfanin koyar da yaro kyawawan halaye da dabi’un Musulunci safe da maraice amma sai ya je wurin miyagun abokan zama da za su rusa abin da iyayensa suka dasa masa? Ko kuma mene ne amfanin koyar da yaro kyawawan dabi’u na shekara da shekaru amma sai wannan mahaifi nsa ya kai shi muhallin da yake cike da almundahana?
Kuma kafin Imam Malik ya zauna ya fara bayar da fatawa said a manyan malamai saba’in suka tabbatar da cancantarsa a kan haka. Ku dubi bambancin da ke tsakanin wanda yake yabon kansa kuma yake cusa kansa a san da shi da wanda iliminsa ya jawo masa yabo kuma ya kai shi cikin zababbun mutane. Imam Malik (Rahimahullah) ya ce: “Ba kowane mutum da zai so ya zauna a masallacin ya koyar da Hadisi kuma ua bayar da fatawa ba ne ya cancanci haka. Mai son ya zauna ya bayar da fatawa ya fara da neman shawarar salihai da zababbun mutane; idan suka ga ya cancanci haka sai ya fara; domin ni ban zauna in fara koyar da Hadisi ko in bayar da fatawa ba, sai da malamai saba’in suka tabbatar da cancantar yin haka.”
Imam Malik ya ce: “Ni mutum ne kawai, nakan yi kuskure kuma nakan bayar da fatawoyi daidai. Idan na bayar da fatawa ku auna su, idan sun dace da Sunnah ku karbe su.” Da wannan muhimmmin bayani, Imam Malik ya nuna madaidaiciyar hanya ta bi a tsakanin masu yin makauniyar biyayya ga shugabanni da wadanda suke watsi da ingantaccen nassi da maganganun malamai, suna cewa: “Su ma mutane ne, mu ma mutane ne.” Mene ne bambancin wadancan mutane da wadannan mutane? Mene ne bambancin mutane da suka rasu wadanda Allah Ya girmama sunansu na karnoni da mutanen da ba su da wata daraja da suke masu rai ne da za a iya kirga su da matattu? Ambaton sunayen wadannan malami na farkar da zukata mutum ya rika jin kamar yana tare da su a zuciyarsa. Wadannan manyan malamai ba ilimi suke da shi kadai ba, a’a su shugabanni ne a fagen kyawawan halaye da hakuri da muru’a da kamun kai da kuma tsoron Allah.
Sai dai kuma akwai wadansu daga cikin mabiya wadannan malamai wadanda suka zabi su takaita kansu a kwaikwayo ba su su son su kara gusawa gaba duk da cewa za su iya bambancewa a tsakanin karya da gaskiya.
Kuma kuskure ne ka rika tozarta ayyukan sauran mutane, ko ka rika jin aikin kirkin wani ya fi na saura. Wannan saboda ilimi da gogewa baiwa ne daga Allah ba daga wani mutum ba. Wannan shi ne babbar fahimtar da Malik yake son nuna wa jama’a cewa yi wa Musulunci hidima aiki ne da ke kan kowane Musulmi a duk bangarorin rayuwa ba tare da wani ya yi tawaye ko adawa ga sauran Musulmi ba. Imam Malik ta rubuta wa wadansu masu ibada a zamaninsa cewa: “Allah Ya karkasa ayyukanmu kamar yadda Ya karkasa baiwarmu (fasaharmu). Wadansu Ya bas u karfin jiki za su iya yi nafilfili masu yawa, amma ba a ba su baiwar yin azumin nafila ba; wadansu kuma an albarkace su da iya yin azumi, wadansu da Jihadi, wadansu da neman ilimi. Yada ilimi yana daya daga cikin kyawawan ayyuka kuma ina jin Allah Ya albarkaci wani da wani abu kuma ba na jin abin da nake yi ya fi abin da kake yi, sai dai fatata dukanmu biyu muna aikata kyawawan ayyuka.”
Domin haka mutane masu bayar da sadaka da wadanda suke tafiyar da rayuwarsu a tafarkin Allah da malamai da masu yada Musulunci da masu yi wa Musulunci hidima ta fannoni da dama duk suna yin aiki na kwarai – idan suka yi da ikhlasi da kyakkyawar niyya.
Duk lokacin da aka tambayi Imam Malik (Rahimahullah), yakan shaida wa mai tambayar cewa: “Ka tafi ka ba ni dama in yi nazari a kanta.” Idan mai tambayar ya tafi, sai almajiran Imam Malik sai su tambaye shi dalilin abin day a yi, sai ya amsa da cewa: “Ina tsoron wata rana (ta haduwa da) Mai tambaya (Allah) kuma wannan ran ace (mai firgitarwa)”
Mutanen Yamma (Maghrib) sun aiki wani mutum ya tambayi Imam Malik (Rahimahullah) a kan wasu abubuwa. Mutumin ya yi wa Imam Malik wata tambaya, amma sai ya ce: “Ban sani ba, domin ba mu san wannan abu ba a nan kasarmu, kuma ba mu ji wani daga cikin malamanmu ya ce wani abu a kansa ba, amma za ka iya sake dawowa.” Washegari mutumin ya koma ga Imam Malik sai Malik ya ce masa: “Ka yi min tambaya amma ban san amsarta ba!” sai mutumin ya ce: “Ya Abu Abdullah! Na zo ne daga wadansu mutane wadanda suke tunanin babu wani mutum a duniya wanda yake da ilimi kamarka!” Sai Malik ya ce: “Ni ma ban cika goma ba.”
Sannan an taba tambayarsa sai ya ce wa mai tambayar ya ba shi lokaci zai yi bincike, sai mutumin ya ce: “Amma ai al’amarin mai sauki ne.” Sai Malik ya ce: “Ai babu wani abu mai sauki a fagen ilimi. Ko ba ka ji fadin Allah ba ne cewa: “Lallai ne Mu, za Mu jefa maka magana mai nauyi.” (k:73:5).
Imam Malik (Rahimahullah) ya kasance yana cewa: “Masu ilimi da fahimta da na iske a kasarmu, idan aka tambayi dayansu kan wani batu, yakan ji kamar zai fadi ya mutu. Amma mutanen zamaninmu su kuma suna son su rika bayar da fatawa (ba tare da damuwa ba). Da sun san abin da za su je su iske a gobe (Ranar Hisabi) da ba su yi haka ba. Umar da Ali da Alkama (Allah Ya yarda da su) suna daga cikin mafifitan sahabban Annabi (SAW), amma duk lokacin da wani ya tambayi daya daga cikinsu sai ya tambaye ’yan uwansa sahabbai kafin ya bayar da amsa a kanta. Amma abin takaici shi ne bayar da fatawa ta zama abin alfahari ga mutanen zamaninmu.”
Wadannan fa fitattu kuma kwararrun masana ne da suka cika duniya da iliminsu da kyawawan ayyukanku, amma duk da haka sukan ce: “Ba mu sani ba.”
Don haka da mamaki ka ga wadansu mutanen da ba su san komai ba game da dokokin Musulunci amma duk da haka suna muzanta su ta hanyar yin magana a kana bin da aka yarda da shi kuma aka halatta. Har ta kai wani batu kan dkar Musulunci kan iya zuwa a lokacin wani taro ba tare da dukan mahalartarsa – tare da bambancin fagen iliminsu – sun bayar da nasu ra’ayoyin ba, misali suna cewa ‘a fahimtata…’ ko ‘bisa abin da nake da yakini…’ da sauransu.
Subhanallah! Yaushe al’amarin halattawa da haramtawa ya zamo wani batu na tattaunawar jahilci da ra’ayi?
Idan aka ce Injiniya ya zamo likita ya rika ba mutane magunguna, me za ku ce a kansa, kuma mene ne zai kasance makomarsa? To mene ne makomar mutumin da ke caccakar dokar Musulunci ya rika magana a kan halattawa da haramta abubuwa ba tare da ilimi ba, musamman a muhimman abubuwa da idan Umar (Allah Ya yarda da shi) ne lamarin ya zo masa sai ya tara dukan sahabban da suka halarci Yakin Badar su taimaka masa wajen warware matsalar.
Amma abin takaici bayar da fatawa a zamaninmu ya zamo wani fage da duk wanda yake son ya yi suna ko yake neman girmamawar mutane zai fito ya bayar da ita koda za ta sa Allah Ya fusata da shi.
’Yan uwa a cikin imani! Batutuwan da suka shafi imani a Musulunci abubuwa ne da ba su bukatar wani ya bayar da wani ra’ayi nasa na daban. Kuma haka batutuwan da suke da madogara daga Alkur’ani da Sunnah ko wanda malamai suka yi ittifaki a kai.
Kuma wajibi ne a kan dukan Musulmi su bar masana su yi magana a kana bin da ya shafi ilimi, kada su shiga batun da ya shafi halal da haram alhali ba su da ilimi a kai.
Imam Malik (Rahimahullah) ya ce: “Duk wanda yake son ya bayar da amsa a kan wata tambaya, to ya bijiro da kansa cewa yana tsaye ne a tsakanin wuta da Aljanna, ya tsaya ya yi tunani kan yadda zai kubuta a Ranar kiyama kafin ya bayar da amsar.”
Wadansu mutane sun dauka wadancan malamai sun kware ne kawai wajen al’amuran da suka shafi sabani da tattauna batutuwan da suka shafi ilimi, kuma zamaninsu sun rika sukar Hadisan da suke gyara zukata su tunatar kan Aljanna da wuta. Domin a san cewa zamaninsu ya hada fagagen ilimi daban-daban, bari mu ji abin da Imam Malik ya ce ga wani dan uwansa da yake sukarsa: “Ka tunatar da kanka kan zafin mutuwa da abin da za ka hadu da shi da abin da zai zamo makomarka bayan ka mutu; da tsayuwarka a gaban Allah da hisabin da za a yi maka da koma makomarka ta karshe Aljanna ko wuta. Ka yi shiri ga wannan lokaci kan yadda za ka samar da sauki ga kanka a lokacin, domin lokacin za ka ga abin da zai samu wadanda suka ja wa kansu fushin Allah da figircin irin bala’in da suke ciki, za ka ji kukansu a cikin wuta da bakaken fuskokinsu, ba su iya gani ko magana, za su rika kururuwar hallaka, kuma abu mafi girma daga haka, Allah zai kawar da kanSa daga gare su, za su yi ta neman Ya ba su amsa kan kukansu amma sai Ya ce: “Ku tafi (da wulakanci) a cikinta, kada ku yi Mini magana.” (k:23:108). Idan ka san wadannan duka, babu wani abu a wannan duniya da zai kasance babba gare ka da ba za ka sadaukar da shi domin neman ceto a Lahira ba.”
Imam Malik ya yi jinya na kwana 22 kuma ya rasu yana da shekara 87. Fitaccen almajirinsa, Nafi’u ya ce: Malik ya rasu yana da shekara 87, kuma ya rayu a Madina yana matsayi Muftinta na shekara 60.”
Ya Allah! Ka yi rahama ga Imamu Malik wanda ya ce: “Na iske wadansu mutane a Madina wadanda ba su da wasu laifuffuka amma suna maganganu a kan laifuffukan wadansu mutane, don haka sai mutane suka kirkiro musu laifuffuka. Kuma na iske wani rukuni na mutane a Madina da suke da laifuffuka amma suka guje wa yin magana kan laifuffukan sauran mutane, sai mutanen su ma suka kame daga yin magana a kan laifuffukansu.”