✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wane ne sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya?

A yau din nan ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami tsohon Sakataen Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawan, sannan ya nada Mustapha Boss domin ya…

A yau din nan ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami tsohon Sakataen Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawan, sannan ya nada Mustapha Boss domin ya maya gurbinsa.

Ganin cewa Mustapha Boss ba sananne bane, shi ya sa Aminiya ta rairayo takaiccen bayanai a kan sabon sakataren Gwamnatin.

Shi dai Mustapha Boss dan asalin Jihar Adamawa, da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

An haifeshi ne a garin Hong. Sannan kuma kwararren lauya ne, inda har ya taba zama shugaban Kungiyar Lauyoyi (NBA), reshen Jihar Adamawa.

Ya fara harkar siyasa ne a Jam’iyyar SDP, inda har ya rike shugaban jam’iyyar na tsohuwar Jihar Gongola tsakanin shekarar 1990 zuwa 1991, kamar yadda kafar yada labarai na Daily Nigerian ta ruwaito.

Mustapha ya tsaya tsakarar Gwamnan Jihar Adamawa a shekarar 1991 a karkashin Jam’iyyar SDP.

Hakanan kuma, Mustapha ne mataimakin shugaban  tsohuwar Jam’iyyar ACN tsakanin shekarar 2010 zuwa 2013, wadda daga bisani ta dukule da wasu jam’iyyu suka kafa Jam’iyyar APC mai mulki yanzu. Sannan kuma shi ne mataimakin shugaban yakin zaben shugaban kasa na jam’iyyar ta ACN a shekarar 2007.

Bayan an kafa Jam’iyyar APC, Mustapha ya kasance daya daga cikin jigogin jam’iyyar, inda ya kasance daya daga cikin ‘yan kwamitin karbo mulki, sannan kuma har yanzu memba ne a kwamitin amintattun jam’iyyar ta APC.

Kafin a nada shi sabon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mustapha ne shugaban Hukumar National inland waterways Authority (NIWA).