✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wanda yake yi wa Nura M. Inuwa sojan gona ya shiga hannu

A ranar Litinin da ta gabata ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta gurfanar da wani matashi dan shekara 25 mai suna Umar Abdulhamid a…

A ranar Litinin da ta gabata ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta gurfanar da wani matashi dan shekara 25 mai suna Umar Abdulhamid a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge a birnin Kano bisa zarginsa da laifin sojan-gona da zamba cikin aminci da kuma karya da yaudara.
Matashin wanda aka fi sani da  dan Kwalisa mazaunin Unguwar Sheka ne a birnin Kano, kuma an tuhume shi ne da yin sojan-gona da aikata zamba cikin aminci ta hanyar yin shiga irin ta mawaki Nura M.  Inuwa, sannan ya rika zuwa wurare daban-daban yana karbar makudan kudade da sunan zai yi musu waka.
A lokacin zaman kotun dan sandan mai gabatar da kara ya bayyana cewa dan Kwalisa yakan je wurin taro ko biki ko suna a ciki da wajen Najeriya da sunan shi ne mawaki Nura M. Inuwa, inda wani lokaci da zarar kudin da aka yi cinikin za a ba shi ya shiga hannunsa, ba za a kara ganinsa ko a same shi ta waya ba, kuma hakan ya rika jefa mawaki Nura M. Inuwa cikin matsala.
Matashin da ake tuhuma ya amsa laifinsa, inda alkalin kotun Mai shari’a Nasiru Abba Magashi ya tura shi kurkuku don zaman jirar hukunci.
Binciken da Aminiya ta gudanar ta gano cewa asirin matashin ya fara tonuwa ne jim kadan bayan dawowarsa daga Jamhuriyyar Nijar, inda ya kulla wani ciniki da sunan shi ne Nura M. Inuwa, kuma mutanen Nijar din suka biyo shi da Naira dubu 200 don su ba shi a matsayin kudin wakar da zai yi musu, sai dai kafin su samu Nuran na bogi ne sai suka fara haduwa da Nura M. Inuwa na gaskiya, daga nan aka kafa masa tarko a karshe aka kama shi a garin Wudil da ke Jihar Kano.
Bayanan da Aminiya ta samu sun nuna cewa an taba kama matashin a Abuja a baya, amma a wancan lokacin mawaki Nura Inuwa ya yi masa afuwa bayan ya yi alkawarin ba zai maimaita hakan ba.
A yanzu dai Mai shari’a Nasiru Abba ya dage sauraren karar zuwa ranar Alhamis 8 ga Satumba, 2016.
A tattaunawar da mawakin ya yi da Aminiya bayan zaman kotun ya bukaci mutane su rika zuwa ofishinsa don kulla huldar cinikayya, ba kawai su rika magana da wadansu ta waya ba, sannan su rika yarda cewa sun yi magana da Nura M. Inuwa ba.
Mawaki Nura Inuwa ya ce a lokuta da dama an sha zuwa wurinsa cewa an zo karbar wakar da bai san da ita ba, “Kuma da yawa ina cikin harkokina sai in ji an kira ni a waya ko a riske ni a situdiyo a ce mini an zo karbar waka, wadannan mutane sukan zo daga garuruwa daban-daban, nakan sanar da su ban san da maganar ba, amma sai su ce sun yi magana da ni ta waya, idan na tambaye su lambar da suka yi magana da ni sai su nuna mini wata lamba daban, daga baya dai su fahimci an damfare su ne. Irin wannan al’amari ya faru da ni bila adadin, kuma al’amarin na ci min tuwo a kwarya,” inji shi. A karshe ya bukaci masu sojan-gona da zamba cikin aminci su ji tsoron Allah, su fahimci ko ba dade ko ba jima asirinsu zai tono, kuma doka za ta yi aiki a kansu.
Amfani da sunan ’yan fim domin aikata laifi ko yin damfara da zamba cikin aminci ya fara zama ruwan dare domin a kwanakin baya ma, jarumi Adam A. Zango ya kama wadansu mutum uku da ke amfani da sunansa suna neman mata. Haka wani matashi ya rika amfani da sunan jaruma Jamila Nagudu wajen yin damfara, inda shi ma dubunsa ta cika aka kama shi.