✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wanda ya yi fyade ga tsohuwa mai shekara 80 zai shekara uku a kurukuku

Wata Kotun Majistare da ke garin Modakeke a Jihar Osun, ta daure wani mai suna Jimoh Oyeyemoni shekara uku a kurkuku, sakamakon samunsa da laifin…

Wata Kotun Majistare da ke garin Modakeke a Jihar Osun, ta daure wani mai suna Jimoh Oyeyemoni shekara uku a kurkuku, sakamakon samunsa da laifin yi wa wata tsohuwa mai shekara 80 fyade.

Mai gabatar da kara Sufeta Ona Glory, ta shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata fyaden ne a ranar 23 ga Disamban da ya gabata da misalin karfe 2:30 na rana, a kauyen Onibambu, kusa da garin Modakeke.

Ta ce Jimoh ya afka wa tsohuwar mai shekara 80 mai suna Sogunlana a cikin gonarta, inda  ya yi mata barazanar kisa idan ba ta amince ya yi lalata da ita ba.

Bayan sauraron dukan bangarori da kuma shaidu, alkalin kotun Mai shari’a A. O. Famuyide ya daure Jimoh shekara uku ba tare da ba shi zabin biyan tara ba, domin hakan ya zama ishara gare shi da sauran batagari irinsa.