✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wanda bai ji bari ba

Barka da warhaka Manyan Gobe Ina fata kun dawo hutun makaranta cikin koshin lafiya. Duk da kasancewar wannan makon aka koma makaranta yana da kyau…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Ina fata kun dawo hutun makaranta cikin koshin lafiya. Duk da kasancewar wannan makon aka koma makaranta yana da kyau ku fara karatu da wuri, domin masu magana na cewa da zafi-zafi akan bugi karfe.
A wannan makon na yi muku guzurin labarin ‘Wanda bai ji bari ba’. Ina fata za ku karanta labarin don kwasar darussan da ke cikinsa.
A sha karatu lafiya:
Naku Kawu Bashir Musa Liman

Wanda bai ji bari ba

A wani lokaci a kasar Gabas an yi wata tunkiya da ‘yarta marar jin magana. A kullum takan rika ba ta shawara da yi mata hannunka mai sanda a kan rayuwar duniya amma sai ta rika kekasa-kasa. Duk da haka ba ta hakura wajen yi mata nasiha ba.
Babban abin da yake bata wa tunkiya rai shi ne yawon da ‘yarta take yi, inda wani lokaci sai an rika fita nemanta.
“Duk wanda ba ya jin maganar iyaye, ko ba ya biyayya ga na gaba da shi to karshensa ba zai yi kyawu ba. Sau da dama ina gargadinki kan fita yawo amma ba kya ji ko? Duniyar nan yanzu ta baci, ba ki san da wanda za ki gamu da shi ba. Ka yi taka tsan-tsan ma yaya ka kare, ballantana ba ka yi ba. Don haka ina fata za ki daina fita yawo, ki kuma kasance mai jin maganata.” Tunkiya ta fada wa ‘yarta, amma hakan bai sanya ta natsu ba.
Hakan ne ma ya sanya bayan tunkiya ta zagaya, sai ta fita. Ta yi ta tafiya har ba ta son ta shiga daji sosai ba. Bayan ta gaji tikis ne sai ta karasa wata korama don ta sha ruwa, ana cikin haka sai dila ta iso don ta sha ruwa, a nan ta ga ‘yar tunkiya sai kwadayi ya kama ta.
Ganin dila ne ya sanya ta tsorata sannan ta shiga gudu, dila ta bi ta a guje bayan ta kure mata gudu, ta kama ta sannan ta cinye ta.
Hakan ne ya sanya masu magana suke cewa duk wanda bai ji bari ba zai ji hoho