Malam Shehu Bukar wanda aka fi sani da sunan Bukar T, wani mai sayar da kaset ne da ke Kasuwar Barci a garin Kaduna. Dattijon ya yi suna ne wajen tattara tsofaffin faya-fayan mawakan Hausa, musamman na Dokta Mamman Shata Katsina. Aminiya ta tattauna da shi kwanakin baya. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ko za ka fada mana tarihinka?
Bukar T: Assalamu alaikum sunana Shehu Bukar, amma an fi sanina da Bukar T. An haife ni a garin Maiduguri da ke Jihar Barno, a ranar 30 ga watan Afrilun shekarar 1950, amma ni mutumin Sapele ne. Na yi karatun firamare da na addini. Kuma akalla ina jin harsuna guda takwas, ciki har da Hausa da Tutanci da Yarbanci da Ibo da yaran Tibi da Idoma da Gwandara da sauransu. Wannan ba ya rasa nasaba da yadda na kewaye bangarorin kasar nan daban-daban.
Sunan Bukar T ya samo asali ne tun lokacin da muke yara, saboda akwai wani mawaki Ba’amurke, wanda ake kira da Booker T. & the M.G.’s wanda kuma yake salon kidan Jazz Music. Saboda yadda muke shaukin wakokinsu daga nan sai mutane suka fara kirana da sunan Bukar T. Har ila yau, harafin “T” ya samo tushe ne daga sunan kakana Uteeh, amma ni sai na cire harafin farko da na karshe wato “U” da “h”, sai sunan ya zama Tee.
Aminiya: Me ya ja hankalinka zuwa aikin soja?
Bukar T: Wannan ya faru ne a lokacin yakin Basasa lokacin ina garin Makurdi. Akwai wata rana da La’asar muna cikin kasuwa sai wadansu sojoji suka zo suka fara kama mutane don tilasta musu shiga aikin soja. Daga nan sai na yanke shawarar shiga aikin. Akwai wani lokaci a Enugu, muna aiki a bangaren sadarwa, wanda marigayi Murtala Muhammad yake shugabanta. Kuma saboda sojojin Najeriya sun kwace kayayyaki daga mutanen Biyafara ciki har da kayan kade-kade. Wannan ya sa idan muka zauna da yamma, kamar wasa sai mu fara yin amfani da kayan kidan tare da rera waka. Ana nan, ana nan sai aka ce a fidda gwanaye a cikinmu. Kuma a cikin wadanda aka zabo har da ni, inda aka ba ni mukamin manajan ’yan wasa. Haka dai muka fara wasa a lokacin muna gidan soja, kuma ba mu fasa ba har bayan lokacin da muka bar aikin soja, wato lokacin da aka kawo karshen yakin Biyafara ke nan. Daga nan ne sai aka dawo da mu Kaduna.
Aminiya: Me ye ya sa ka fara adana wakoki musamman na marigayi Dokta Mamman Shata?
Bukar T: Karambani ne ya sanya ni fara tattara wakoki. Da farko ba wai na dauke yin hakan a matsayin sana’a ba ne. Saboda kafin hakan duk wata sabuwar waka idan ta fito kasuwa, muna saya domin mu je mu zauna mu saurari yadda aka yi kidanta. Daga nan sai mu je mu kada wakar daidai kamar yadda wanda ya yi wakar ya yi kayansa. Tun a wancan lokacin na fara tara faya-fayan mawaka daban-daban. Kodayake, sai da na tara kasa-kasai da dama domin a lokacin sun haura guda dubu. Na fara tattara faya-fayan ne a shekarar 1976 da wakokin irin na Disco da Sentimental da Rege, amma ban dauke hakan a matsayin sana’a ba. Sai dai kawai domin ina sha’awar abin. Da farko na bude shagon daukar hoto ne, amma da tafiya ta yi tafiya sai na fahimci ba na samun riba kamar yadda ya kamata. Daga nan sai na fara tunanin wace sana’a ce zan runguma. Sana’ar da ta fara kwanta mini a rai ita ce ta sayar da kaset. Na fara bude shago a Unguwar Sanusi kafin in bude a nan Kasuwar Barci, wanda daga ne na fara samun daukaka.
Mutane daga nesa da kusa suka dinga tururuwa zuwa shagona domin sayan kasa-kasai. Saboda ina tsintar masu dadi ne, na hada a kaset guda abin da aka fi sani da Selection. Yana da kyau a fahimci cewa wadannan wakokin da nake magana irin na Turawa ne, ba namu na gida ba. Kodayake, lokacin da kaset din bidiyo ya fito na shiga tattarawa kasa-kasan tarihin Najeriya da na yakin Basasa da wasannin Magana Jari Ce da sauransu. A shekarar 1985 da na dawo Kasuwar Barci, sai na fi mayar da hankali a kan faya-fayan bidiyo saboda a lokacin shigo da kasa-kasan rediyo daga kasashen waje yana da wahala. Wata rana muna zaune da wani abokina bayan shekara daya da bude shagon, sai yake ba ni shawara kan me zai hana in dinga sanya wakokin Shata da Oumou Sangaré da dan Kwairo da sauran makadanmu na gida. Sai na karba shawararsa. Da wakar Shata na fara gwadawa, inda a ranar kasuwa ta bude mini sosai, na samu Naira 650 madadin 200 da nake samu duk rana. Daga nan sai aka fara tambayar wakoki kamar na su dan Anace. Fahimtar abin da jama’a ke bukata ya sa na dinga tare duk masu sayar da kaset din garin nan domin samun irin faya-fayan da ba ni da su daga wurinsu. Bayan na samu kuma sai na kara inganta nawa ta hanyar kara daukarsu da babbar na’ura, saboda haka nawa sai ya bambanta da na su wajen ingancin sauti. Daga nan sai masu sayen da kansu suka dinga kawo mini wadansu mutanen. Sai kasuwa ta kara bude mini inda a rana nakan hada kudin da ya kai Naira 1500 ta wancan lokacin. Wannan ya sa na kara ba da kaimi sosai. Haka dai na dage wajen tattara faya-fayan Shata da dan Maraya Jos da dan kwairo da dan Anace da Sani Sabulu da Jan Kidi da sauran mawaka da dama.
Aminiya: Ta wace hanya kake samun tsoffin faya-fayan?
Bukar T: A gaskiya tattara wadannan faya-fayan aiki ne sosai saboda wadansu faya-fayan ba a samunsu a kaset. Hakan ya sa na dinga zuwa kasuwannin garuruwa daban-daban domin neman faya-fayan garmaho a wajen ’yan gwangwani wadanda daga bisani nake mayar da fya-fayan zuwa kaset. Akwai kuma lokuta da dama da idan aka raba wa magada kayayyakin gado nakan sayi tsofaffin faya-fayan daga gare su, wanda su magadan galibi ba su san darajarsa ba. Na dade ina wannan. Kuma har yau ina ci gaba da tattara wadannan tsofaffin faya-fayan, musamman na Shata. Mukan mayar da faya-fayan daga garmaho zuwa kaset, a yanzu kuma zuwa sidi ko kuma Memory card.
Aminiya: Faya-fayan Shata nawa kake da su a yanzu?
Bukar T: Wallahi ba zan iya sani ba. Musamman ma saboda har yanzu kara samunsu muke, amma a gaskiya suna da dama.
Aminiya: Mene ne bambancin kadekadenmu na Hausa da kuma na Yammacin Duniya?
Bukar T: A gaskiya kawai bambanci saboda namu na Hausa ya fi ilmantarwar, na Turanci kuwa abu biyu kawai ya kunsa, wato saurayi da budurwa. Ka ga idan zan ba da misali da wakokin Shata, makaranta ce. Na fadi haka ne saboda dimbin ilimin da darussan da suke kunsa. Wannan ya sa hatta malaman addini sukan nufu nan domin neman wakokinsa. A gaskiya a duka duniyar mawaka ba mawaki kamar Shata. Amma idan maganar wakar sarauta ce, to babu kamar dan kwairo. Shi kuma Shata a nashi bangaren zai yi wa Basarake waka, zai yi wa talaka waka, kai Shata zai yi wa kowane mahaluki waka. Wani karin abin sha’awa da Shata shi ne idan a yau zai yi maka waka, gobe kuma ya maimaitata, to za ka ji ya kara kayatata fiye da yadda ya yi ta a baya.
Aminiya: Wadanne manyan mutane za ka tuna sun taba tuntubarka domin neman wakokin Shata?
Bukar T: A gaskiya suna da dama, amma bai kamata na kira sunansu ba. Saboda wata kila ba za su ji dadi ba. Cikinsu akwai gwamnoni da sarakuna da sauransu. Nakan samu kiran waya daga wurare daban-daban, hatta daga kasashen ketare, inda za ka ji mutum ya bukaci in tanadar masa faya-fayai da ba a ko’ina ake samunsu ba.
Aminiya: Yaushe ka fara haduwa da Shata?
Bukar T: Mun fara haduwa ne a cikin shekarar 1972, lokacin za mu je wani wasan rawa da aka gudanar a Jihar Kano.
Aminiya: Akwai wani abin mamaki da za ka tuna Shata da shi?
Bukar T: Akwai wata rana da Shata zai yi wani wasa a Funtuwa, a wani otel mai suna bictory Hotel. Ana cikin shirye-shiryen ne sai wani maroki ya hango Shata yana zuwa. Kodayake mun fara ganin shi kafin shi. Abin mamakin da ya faru shi ne a daidai lokacin da Shata ya iso wurin wasan da motarsa kirar Marsandi tare da wani dan sanda. Sai duka marokan nan suka rugo a guje zuwa wajensa, isarsu ke da wuya, sai marokan nan daya bayan daya suka kwanta a gaban kofar motar da Shata zai fito, inda kowane ya shinfide hannun babbar rigar da yake sanye da ita a kasa domin Shata ya taka ya isa dandalin wasan. Ba tare da ya taka kasa ba. Kuma suna daga kwance suna masa kirari. A gaskiya tun da aka haife ni ban taba ganin haka ba, sai a wannan ranar. Abin ya yi matukar ba ni mamaki.
Aminiya: Kamar wace wakar Shata ka fi kauna?
Bukar T: Akwai wata waka da ya yi wa wani ana kiransa Audu Mai Jinka, a gaskiya ita ce na fi so. Kuma na fi kaunar wannan wakar ce saboda yadda ya yi Hausa sosai a cikinta.
Aminiya: Kana da yara wadanda kake koya masu wannan sana’ar?
Bukar T: A’a. Saboda duka yarana suna zuwa makaranta ne. Mutane suna yawan jan hankalina kan in ci gaba da dagewa kan wannan sana’ar, amma gaskiyar al’amari shi ne ba ni da wani wanda idan yau ba ni zai ci gaba daga wurin da muka tsaya. Idan ka lura yaran yanzu ba su da hakuri da juriya. Ina da fatan samun magaji, amma matakin farko shi ne sai ya kasance yana da ra’ayin sana’ar.
Aminiya: Me ya sa ba ka adana wakokin zamani wato irin na fina-finan Hausa?
Bukar T: Ba na ajiyewa su ne saboda yadda ba sa kunshe da al’adun Hausa. Yawancin fina-finan suna kwaikwayon salon labaran fina-finan Indiya ne. Amma na adana irin fina-finan Hausa na farko kamarsu Daskin da Ridi da Sangaya da sauransu, saboda irin ma’anar da suke dauke ita.
Aminiya: Kana da wani kira ga mawakan Hausa na zamani?
Bukar T: Ba wani kira da nake da shi a gare su . Zamani ne irin nasu. Ko ka ba su shawara ba saurara za su yi ba. Idan ka yi magana sai su ce gafara can mutumin da. Abin tsoron shi ne kayayyakin kidanmu na da, suna neman bacewa.
Aminiya: Wace fa’ida ka samu albarkacin wannan sana’ar?
Bukar T: Alhamdulillah, a cikinta na gina gida, na sayi mota.
Aminiya: Ko akwai wani kalubale da kake fuskanta?
Bukar T: Babban fatanmu shi ne ranar da babu mu. Faya-fayanmu a adana su domin amfanin jikokinmu. Kuma babban burina shi ne na cika da kyau da imani.
Aminiya: Ya batun iyali fa?
Bukar T: Ina da mata daya da ’ya’ya biyar da kuma jikoki da dama.