Marubuci A. Y. HUSAIN (JUSTICE AYAH), U/MU’AZU KADUNA (08064847041) ya bi kadin muhimmancin godiya a cikin al’amuran yau da kullum na jama’a, don haka ya kattaba want ton gajerar waka, yana cewa:
In dai amma ka yi godiya
Koda sharri ka yi godiya.
Jalla sarki ya wahadaniya,
Sunanka na fara, godiya.
Sai salati ga hairul ambiya,
dan Aminatu mai yin godiya.
Taken wakar tau dai a yau,
Jama’a mu zan yin godiya.
Sunan wakar ma dai haka,
Ni na yi ta na sa mata godiya.
Wata ’yar nasiha za na yi,
In kun ji ku yo min godiya.
Ka ga koda mene an ka ma,
Wallahi ka zam mai godiya.
Da kudinka ka bayar an ka ma,
A hakan daidai ka yi godiya.
Babur da ka hauwa kabbiya,
In ka sauka ka yi mai godiya.
Ko gidan mai ne ka saye shi mai,
Kar ka fige ba wata godiya.
Shoeshiner ya ma aikinka tsaf,
Ba shi moni kai masa godiya.
Mai tumatir bayan kin saya,
Da kudinki ki yi masa godiya.
Mai yankan farce dan halas,
Ba shi Naira kai mai godiya .
Mai aski shi ma in ya ma,
Kar ka bar shi ka yi mai godiya .
Kin sai jaka har kin biya?
Mai shagon ki masa godiya.
Kin hau mota kin ban dala,
Why not kuma ki min godiya?
Ko a shago ka sayi biskit,
An ba ka ka yi masu godiya.
Magana in dai nai maka min,
To dole na yi maka godiya.
Kar kudi su hana mana godiya,
Ai biya nai ban yin godiya.
A’aha! Da ya ki ya ba ka fa?
Don Allah mu zan yin godiya .
Bissalamu a nan zan dakata,
’Yar nasiha nai ku yi godiya.
Naku ne Justice AYAH Aleey,
Ko ku ce mini mayen godiya.