✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wajibi ne a sake binciken batar kudin mai dala biliyan 20 – Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce rahoton da kamfanin bincike na PricewaterhouseCoopers(PwC) ya fitar game da badakalar da ke kamfanin man fetur…

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce rahoton da kamfanin bincike na PricewaterhouseCoopers(PwC) ya fitar game da badakalar da ke kamfanin man fetur na kasar wato NNPC, ya nuna cewa kamfanin na da hannu dumu-dumu cikin cin hanci a Najeriya kuma wajibi ne a sake binciken batar kudin mai dala biliyan 20, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana jiya Alhamis.

Sarki Sanusi, wanda shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya sallama daga shugabancin Babban Bankin kasar (CBN) bayan ya yi zargin cewa NNPC bai sanya kudin mai dala biliyan 20 a asusun bankin ba, ya bayyana haka ne a wata wasika da aka wallafa a jaridar Financial Times.
Ya kara da cewa rahoton PwC bai wanke kamfanin man daga zarge-zargen badakala ba, sabanin ikirarin da ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke, ta yi cewa an wanke kamfanin NNPC daga zarge-zargen.
Shi dai rahoton na PwC ya ce ana cuwa-cuwa sosai wajen biyan kudin tallafin man fetur da kalanzir.
Kamfanin PwC ya ce a wasu lokutan NNPC na biyan kamfanoni kudin tallafin man fetur sau biyu.
Masu binciken sun ce akwai bukatar a yi wa dokar da ta kafa NNPC garanbawul domin tabbatar da cewa dukkanin kudaden da kasar ke samu daga sayar da danyen mai na shiga asusun gwamnatin tarayya kai-tsaye.
Rahoton na binciken kuma ya bukaci NNPC ya mayar wa gwamnatin Nigeria kusan dala biliyan daya da rabi saboda kin saka wasu kudi da aka sayar da man fetur.