✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Waiwayen Harkokin Wasanni A Shekarar 2013: Aled Ferguson ya yi ritaya

Kocin Manchester United Sa Aled Ferguson ya yi ritaya daga kocin kulob din a wata sanarwar da aka fitar a shekaranjiya Laraba.Sanarwar ta ce kocin…

Sir Alex FergusonKocin Manchester United Sa Aled Ferguson ya yi ritaya daga kocin kulob din a wata sanarwar da aka fitar a shekaranjiya Laraba.
Sanarwar ta ce kocin zai yi ritaya ne a jibi Lahadi a ranar da ake sa ran kulob din zai daga kofin gasar Premier da zarar sun gama wasan karshe da kulob din West Brom Albion.
Ferguson ya shafe kimanin shekara 27 ne yana kocin kulob din kuma ya samu nasarar lashe kofuna 49.
dan kimanin shekara 71, Ferguson ya sha nanata cewa ya kusa yin murabus daga koci a ‘yan shekarun baya.  Abin mamaki shi ne a wannan karo babu zato ba tsammani sai aka wayi gari da sanarwar cewa kocin ya ajiye aiki.