A yanzu wata shida ke nan da bullar cutar coronavirus a Najeriya bayan bullarta karon farko a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020.
Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da bullar cutar wadda ake kira COVID-19 a karon farko a Jihar Legas.
Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ce ta tabbatar da bullar cutar cikin wani sako da ta wallafa a Twitter, inda ta ce a karon farko an samu bullar bakuwar cutar a Najeriya tun bayan barkewarta a China a watan Nuwamban 2019.
Hakazalika Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC), ta wallafa a shafinta na Twitter cewa Ministan Lafiya na ya tabbatar da bullar cutar a Jihar Legas.
Cikin sanarwar da Ministan, Dakta Osagie Ehanire ya fitar ya ce wani bako daga kasar Italiya da ke aiki a Najeriya ne ya shigo da cutar bayan ya taso daga birnin Milan kuma ya sauka a birnin Ikko.
Tun daga wannan lokacin gwamnatin kasar ta ke fadi-tashin dakile yaduwar cutar, waddda a halin yanzu babu Jihar da ba a samu bullarta ba.
Bayanai daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa Najeriya ce kasa ta uku cikin jerin kasashen da aka samu bullar cutar a nahiyyar Afrika bayan Masar da Aljeriya.
Alkaluman da NCDC, ta saba fitarwa duk rana, sun nuna cewa daga bullar cutar a kasar yanzu mutum 53,317 ne suka harbu.
Bayanan NCDC sun nuna cewa mutum 40,726 ne suka warke daga cutar bayan kamuwa, yayin da mutum 1,011 suka riga mu gidan gaskiya.
Kididdigar da Hukumar ta fitar a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, ya nuna cewa mutum 11,580 suka rage dauke da kwayoyin cutar a fadin kasar.
Ga kididdigar alkaluman da NCDC ta fitar kan cutar a kowacce daga cikin jihohi 36 na kasar da kuma birnin Abuja da cutar ta bulla:
Jihohi | Kamuwa | Masu dauke da cutar | Warkewa | Mutuwa |
Legas | 18,056 | 2,606 | 15,227 | 202 |
Abuja | 5,094 | 3,561 | 1,468 | 50 |
Oyo | 3,091 | 1,204 | 1,819 | 37 |
Edo | 2,555 | 192 | 2,263 | 100 |
Filato | 2,330 | 1,029 | 1,187 | 29 |
Ribas | 2,128 | 141 | 1,910 | 57 |
Kaduna | 2,098 | 211 | 1,862 | 12 |
Kano | 1,722 | 161 | 1,507 | 54 |
Delta | 1,730 | 133 | 1,540 | 46 |
Ogun | 1,637 | 145 | 1,462 | 26 |
Ondo | 1,524 | 188 | 1,305 | 31 |
Inugu | 1,142 | 223 | 852 | 21 |
Ebonyi | 971 | 17 | 921 | 27 |
Kwara | 950 | 180 | 740 | 25 |
Katsina | 771 | 290 | 457 | 24 |
Osun | 775 | 85 | 670 | 16 |
Abiya | 759 | 83 | 669 | 7 |
Borno | 740 | 41 | 663 | 36 |
Gombe | 722 | 87 | 609 | 23 |
Bauchi | 658 | 84 | 547 | 14 |
Imo | 526 | 323 | 192 | 11 |
Binuwai | 451 | 301 | 141 | 9 |
Nasarawa | 427 | 117 | 298 | 12 |
Bayelsa | 378 | 26 | 331 | 21 |
Jigawa | 322 | 3 | 308 | 11 |
Akwa Ibom | 277 | 43 | 220 | 8 |
Neja | 241 | 59 | 168 | 12 |
Ekiti | 249 | 104 | 130 | 4 |
Adamawa | 217 | 43 | 159 | 15 |
Anambra | 207 | 30 | 159 | 18 |
Sakkwato | 158 | 4 | 138 | 16 |
Kebbi | 92 | 2 | 82 | 8 |
Taraba | 87 | 9 | 73 | 5 |
Kuros Riba | 82 | 4 | 70 | 8 |
Zamfara | 78 | 1 | 72 | 5 |
Yobe | 67 | 0 | 59 | 8 |
Kogi | 5 | 0 | 3 | 2 |