✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wainar da aka toya a zaben gwamnan Edo

An daku, an sace takardar sakamakon zabe, 'card reader' ta ki aiki, an sayi kuri'u

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa kai-tsaye a zaben Gwamnan Jihar Edo na yau 19 ga Satumba, 2020. Wakilanmu a Jihar da dalibai da cibiyar PTCIJ ta horas kan binciken kwakwaf za su rika aiko da bayanai da hotuna da za mu rika wallafawa akai-aika saboda ku san wainar irin da ake toyawa a zaben.

A nan muke sallama sai wani lokaci za mu kawo muku labaru kai tsaye.

Za ku iya zuwa kasan wanna shafin domin karanto yadda abubuwan ke gudana tun daga farko. Mun gode.


 • Tattara rahoton zabe

Cibiyar Bunkasa Dimokuradiyya (CDD) ta fara shirin tattara rahoton wucin gadi kan zaben gwamnan Edo daga Abbuja.


An lakada wa mai lura da zabe duka

Wani mai sa ido kan yadda zaben ya gudana ya ce an yi masa dukan tsiya aka kuma fasa wayarsa a rumfar da tsohon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole ya yi zabe.

Kazalika wani dalibi mai koyon aikin jarida shi ma an lallasa shi.


 • An fara tattara sakamakon zabe

Karfe 4:16 aka fara karbar sakamakon zabe a Ohordua, Kamar Hukumar Esan ta Kudu mas Gabas a makarntar Girls Model Secondary School, Ubiaja.


 • An kammala zabe

A Karamar Hukuamr Etsako ta Gabas a Makarantar Firamare  ta Eramha, Okpella 3, Gunduma ta 7, Mazaba ta 5, wasu masu zabe sun yi ta kofari da misalin 3:25 na rana cewa ba su samu damar kada kuri’a ba duk da cewa zaben ya ci gaba.


A Okada Grammar School 1 and 2, Mazaba ta 1 (Okada ta Yamma) Kamar Hukumar Ovia ta Arewa maso Gabas an fara kirga kuri’u.


2:51 na rana aka fara kirga kuri’u a Rumfa ta 12, Mazaba ta 12, Evabareke Grammer School, Mazabar Evabareke Ward, Karamar Hukumar Egor.


Karfe 2:38pm, jami’an INEC sun fara ware takardun kuri’un jam’iyyu da taimakon wakilan jam’iyyu a Karamar Hukumar Esan ta Arewa maso Gabas, Uelen/Okugbe (Gunduma ta 4), Makarantar Firamare ta Okpujie ta 2 (Rumfa ta 3).


Karfe 2.38 na rana aka tantance mutum na karshe da ke kan layi a Gunduma ta 7, Ubiaja, Rumfa ta 9 da ke Makarantar Firamare ta Ihia inda Baturiyar Zaben ta koka sosai cewa matsalar na’urar ‘card reader’ ta sa ba a iya tantance wasu masu zabe ba.

2:40 na rana aka fara kirga kuri’u a Gundumar a Rumfa ta 6 da ta 7.


Har bayan karfe 2:40 ana jefa kuri’a a rumfar zaben Adams Oshiomhole, Rumfa ta 01, Gunduma ta 10 (Iyamho), Karamar Hukumar Etsako ta Yamma.


An dakatar da kirga kuri’u

Da karfe 2:36 na rana, masu zabe da wakilan jam’iyyu sun sa an dakatar da kirgen kuri’u domin hana yiwuwar magudi a Rumfa ta 6, Gunduma ta 2, Karamar Hukumar Ikpba Oka.


 • Wasu sun ci gaba da zabe

An ci gaba da kada kuri’a har bayan karfe 2.36 na rana a Mazaba ta 2 (Fugarll), Mazaba ta 7.

Masu zabe a wurin ba su kiyaye tsarin kariyar COVID-19 ba.


An fara kirga kuri’u

Karfe 2.21 na rana, an fara kirga kuri’un da masu zabe suka jefa a Mazaba ta 5 Udo, Rumfar Zabe ta 4, Karamar Hukumar Igueben.

Karfe 2:30 na rana aka kammala jefa kuri’a a Gundumar Uelen/Okugbe Mazaba ta 5, Rumfa ta 5 da ta 6 da ke Makarantar Firamare ta Okpujie, Kamar Hukumar Esan ta Kudu maso Gabas.

Jami’an zabe sun sossoke takardun jefa kuri’a da ba a yi amfani da su ba kafin daga baya su fara kirga kuri’un da aka jefa.

A Mazabar Egor ta 7, Karamar Hukuamr Egor ma an fara kirga kuri’u.


Rikici ya barke da misalin 11:25 na safe a Mazaba ta 1 ta Ewohimi I, Rumfa ta 007 da ke Makarantar Firamare ta Ologbe, Karamar Hukumar Esan ta Kudu mamso Gabas.

Masu zabe sun saba dokokin zabe idan suka rufe Baturen Zaben wanda ke kokawa kan matsaloli, yayin da wakilan jam’iyyu suka ki bayar da hadin kai.


An yi wa dokar COVID-19 karan tsaye

Zabe ya gudana lafiya a Rumfa ta 5, Mazaba ta 8, Karamar Hukumar Ovia ta Kudu maso Yamma.

Mutane sun fito kwansu da kwarkwansu amma ba a kiyaye ka’idar bayar da tazara da sauran dokokin kariyar COVID-19 a wurin zaben ba.


 • Oshiomhole ya caccaki INEC

Tsohon Gwamnan Edo kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole ya yaba da yadda zaben ya gudana bayan ya jefa kuri’arsa a Rumfa ta 1, Mazaba ta 10 (Uzairue ta Kudu masa Gabas) a Karamar Hukumar Etsako ta Yamma.

Oshiomhole ya yaba da kokarin jami’an tsaro da hadin kan da jama’a suka bayar domin ganin zaben ya gudana cikin lumana.

Sai dai ya bukaci jami’an tsaron da su sa ido domin dakile duk wani yunkurin daba, yana mai cewa akwai rade-radin “bata-gare na shirin tayar da fitina gabanin tattara sakamakon zaben”.

Sai dai ya caccaki INEC da cewa yawancin na’urorin tantance masu zabe a mazabarsa ba sa aiki yadda ya kamata, wanda hakan ke sa zaben yin tafiyar hawainiya.


 • An fara kammala zabe

Masu zabe sun kammala jefa kuri’a a Makarantar Firamare ta Eguare I da ta II da ke Ohorudu, Mazaba ta 4 Rumfa ta 2, Karamar Hukumar Estako ta Kudu maso Gabas.

Baturen zaben Rumfa ta 6, Mazaba ta 9 a Karamar Hukumar Owan ta Yamma ya ce masu zabe da suka hallara sun kammala jefa kuri’a.

Ana jira sai karfe 2.30 na rana za a fara kirgen kuri’u.


Wasu da ake zargi ‘yan daba ne sun tarwatsa masu zabe a Rumfar zabe ta Ogbe a Karamar Hukumar Oredo, inda kowa ya ranta a na kare.


Lami lafiya

Zabe ya gudana cikin lumana a Mazaba ta 7, Ikpoba-Akha da kuma Oredo Mazaba ta 10.


An cafke masu magudin zabe

Jami’an tsaro sun damke wasu mutum uku da suka yi kokarin jefa kuri’a da katin zabe na bogi.

An damke mutanen ne bayan an yi ta kokarin tantance katinan nasu da na’urar ‘card reader’ ba tare da nasara ba.

Lamarin ya faru ne da misalin 12:35 na rana a Makarantar Firamare ta Ezuwarha, Rumfar zaben ta 11, Mazaba ta 4 a Iyowa.


 • Rikici ya barke a rumfar Gwamna Obaseki

Jama’a sun ranta a na kare bayan rikicin ya kaure a rumfar zaben da Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo ya jefa kuri’a.

Rikici ya barke ne bayan takaddama tsakanin wakilan wata jam’iyya inda dayansu ke zargin dayan da ba wa masu zaben kudi a lokacin zaben gwamnan jihar, a Makarantar Mode ta Emokpae da ke Karamar Hukumar Oredo, rumfa ta 4, a Mazaba ta 24.

Tuni dai Obaseki dan takarar jam’iyyar PDP da matarsa suka kada kuri’arsu da misalin 11.48 na safiya kafin daga baya a samu hatsaniyar.


 • ‘Card reader’ ta lalace

Masu zabe sun wargaza layi saboda na’urar tantance masu zabe ta lalace, lamarin da ya sa zaben ke tafiya hawainiya Rumfar zabe ta 3 a Ukalo/Ukpoji, Mazaba ta 7, a Karamar Hukumar Igueben.


 • Sai yanzu aka fara zabe.

Da karfe 12:25 na rana aka fara jefa kuri’a a rumfar zabe da ke Makarantar Sakandare ta Ihogbe, Mazaba ta 5, Rumfar Zabe ta 8 a Karamar Hukumar Oredo.

Zaben na gudana cikin lumana da kiyaye matakan kariya na COVID-19.


Rikicin yadda za a yi zabe 

Rabuwar kai game da yadda za a jefa kuri’a ta haifar da rikici a Rumfa ta 5 da ke Mazaba ta 11, Jattu, Karamar Hukumar Orhionmwon.

Karfe 10:18 komai na tafiya daidai a Rumfa ta 11 da 12, amma an samu rikici a Rumfa ta 13, inda wakilan jam’iyyu suke neman su rika umartar masu zabe game da wadanda za su zaba.

Jami’an INEC sun ki amincewa da hakan, lamarin da  ya haifar da tayar da jijiyoyin wuya.


 • Ana sayen kuri’u

Rahoton wani dalibi mai koyon aikin jarida ya ce wakilan jam’iyyu sun labe a wasu wurare inda suke sayen kuri’u a Rumfar zabe ta 7, Mazaba ta 2, Ewohimi II da ke Makarantar Firamare ta Azagba Ikeken, Karamar Hukumar Esan ta Kudu maso Gabas.

Ya ambato yadda wata mata ke daga murya tana cewa, “ka zaba ka karbi dubu biyar”, ko da yake ba a san jam’iyyarta ba.

Wakilan jami’yyu na taimakon masu zabe wajen kada kuri’arsu a rumfar. (PTCIJ).


 • An ci zarafin dan jarida

11:04 an ci zarafin dalibi mai koyon aikin jarida da wani ma’aikacin sa ido a zaben a Karamar Hukumar Igueben.

An kuma tilasta musu goge bidiyon da suka dauka na wani dan Majalisar Dokokin Jihar da ke rabon kudi amma wani basarake ya ce masa hakan ba daidai ba ne.


Mataimakin Gwamnan Edo ya yi zabe

Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Philip Shaibu ya jefa kuri’arsa a Mazaba ta 11, Rumfa ta 11 da misalin karfe 10:30 na safe.

‘Yan jarida sun tambaye shi game da yananyin zaben, amma ya ce ba zai ce komai ba sai zuwa yamma idan ya kara samun bayanan da suka dace.

Philip Shaibu a lokacin da yake jefa kuri’a a mazabarsa domin neman tazarce.

 • Zabe na gudana cikin lumana.

Da misalin 10:30 na safe, a Rumfa ta 13 zuwa 13 a Mazaba ta 5 da ke Kwalejin Marie Goretti, Karamar Hukumar Ikpoba/Okha, ana tantance masu zabe tare da jefa kuri’a a lokaci guda ba tare da wata matsala ba.

Masu zabe sun ba wa jam’ian INEC hadin kai wurin kiyaye dokokin kariyar COVID-19.


Wakilan jam’iyyu na yi wa tsofaffi zabe

Ana zargin jami’an manyan jam’iyyu da yin amfani da yatsun tsoffin mata da zuka zo zaben wajen dangwala wa jam’iyyunsu kuri’a a Maternitiy, Imiomime, Okpella III, Karamar hukumar Etsako ta Gabas.

 


 • Fada ya kaure a rumfar zabe

10:48 na safe an ba hamata iska a Makarantar Firamare ta Ologhe, da ke Ebelle, Mazaba ta 06, Rumfa ta 07, Karamar Hukumar Igueben.


 • Hatsaniya a rumfar zaben Gwamna Obaseki

Rahotanni sun ce an samu ‘yar takaddama a rumfar zaben da Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya je ya jefa kuri’a.

Tun da sanyin safiya jami’an zabe da sauran jama’a suka yi ta dakon zuwan gwamnan, wanda ya isa wurin bayan karfe 10.20.

Da zuwa gwamnan ya je ya wanke hannunsa bisa tsarin kariyar COVID-19 kafin ya zarce a tantance shi.

Jami’an tsaro sun samu nasarar kwantar da hankalin jama’a kuma komai ya ci gaba yadda ake bukata.


 • Dan takarar APC Ize-Iyamu ya jefa kuri’arsa

Dan takarar jam’iyyar APC a zaben Gwamnan Jihar Edo, Osagie Ize- Iyamu ya kada kuri’arsa a mazaba ta 4, rumfa ta 26 da ke Iguododo a Karamar Hukumar Orhiomwon.

Ize-Iyamu ya ce cewa ya ga kamar mata ba su fita sosai ba, yana kyautata zaton matan da za su fito su kada kuri’a za su fi maza yawa, inda ya ce yana da kwarin gwiwar samun nasara zaben.

Bayan kada kuri’arsa dan takarar ya yaba da yadda hukumar zabe ta kasa (INEC) ke gudanar da zaben cikin lumana’ da kuma kiyaye dokokin kariyar COVID-19.

“Muna ba mutane kwarin giwa su fito rukuni-rukuni domin bin ka’idojin COVID-19 na bayar da tazara”, inji shi, bayan ya yi zaben


 • Gwamna Obaseki ya kada kuri’arsa

Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki ya jefa kuri’arsa a zaben da yake neman wa’adin mulki na biyu karkashin inuwar jam’iyyar PDP inda yake fafatawa da babban da abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu.

Obaseki ya jefa kuri’arsa ce a Makarantar Firamare ta Model Emokpae da ke birnin Benin.

Gwamna Godwin Obaseki da matarsa a rumfar da za su jefa kuri’a

 • Ba a bar nakasassu a baya ba

Malam Yakubu Muhammad da Halima masu fama da lalurar ido sun fito domin su jefa kuri’a a makarantar firamare ta Model da ke Emokpae, Benin.

Wasu masu makanta da suka fito suna bin layin kafin su jefa kuri’a a zaben

 • An yi wa nakasassu da tsofaffi tanadi.

An ba wa tsofaffi da nakasassu kulawa ta musamman sannan aka kebe musu wurin zama domin saukaka musu bin layin zabe a mazaba ta 5, Karamar Hukumar Etsako ta Tsakiya.


 • Kayan zabe sun isa da wuri

8:25 na safe jami’an zaben suka lika jerin sunayen masu zabe, minti biyar kafin lokacin fara zaben a mazaba ta 11 rumfa da 5 (Uzairue ta Kudu maso Yamma) a Karamar Hukumar Etsako ta Yamma (PTCIJ).


 • Dattawa sun fito da karfinsu

Tsofaffi sun fito da kwarin gwiwarsu domin jefa kuri’a a zaben na yau.

An ga wasunsu sun zauna tare da juna a Rumfa ta 8, Mazaba ta 6 da ke Makarantar Firamare ta Egure, Karamar Hukumar Igueben.

Tuni aka bari dattawan su jefa kuri’a a rumfar inda komai na tafiya cikin lumana.

Dattawan da suka fito jefa kuria

 • Takardar sakamakon zabe ta yi batar dabo

Masu zabe sun yi bore bayan takardar rubuta sakamakon ta yi batar dabo bayan an kammala rattaba hannu a kanta a mazaba ta 4, rumfa ta 2, Karamar Hukumar Owan ta Yamma, da misalin karfe 8.53 na safe.

Masu zaben na nuna bacin rai saboda abin da suka kira ko-in-kula da baturen rumfar zaben ya nuna (PTCIJ).


 • Kariyar COVID-19

Masu zabe da jami’ai na bin matakan kariyar COVID-19 a wasu daga rumfunan zaben da wakilan namu suka ziyarta.

Mutane na bayar da tazara tsakaninsu a kan layin zabe, suna sanye da takunkumi sannan akan wanke hannu kanfin a kai ga zuwa a tantance mutum.

Kazalika akan yi feshin magani a kan jerin sunayen masu zaben domin tabbatar da kariyar cutar.

Wani mai zabe na wake hannuwansa a Emokpae

 • An fara jefa kuri’a a wasu wurare 

An fara zaben a mazaba ta 9, rumfa ta 10 mai masu zaben 1191 a Karamar Hukumar Esan ta Kudu maso Gabas, da misalin karfe 8.59 da safe (PTCIJ).

Mazaba ta 9, rumfa ta 10 da ke makarantar firamare da Uzgboha, Karamar Hukumar Esan ta Kudu maso Gabas.

Da misalin 8:45 na safe aka fara tantance masu zabe a Rumfa ta 3, Mazaba ta 2 a Karamar Hukumar Ovia ta Yamma.

 

Tuni an fara tantance masu zabe a Karamar Hukumar Ovia ta Arewa. 

 • Wasu ba su ga sunayensu ba

Baturen zaben rumfar zabe ta 10, mazaba ta 11 a Karamar Hukumar Etsako ta Yamma ya yi wa jerin sunayen masu zabe feshin magani domin kariya daga cutar coronavirus.

AN tuntube shi game da wadanda ba su ga sunayensu a cikin jerin sunayen da aka lika ba, amma ya ce babu abin da za a iya yi a akai. (TPCIJ).

Jerin sunayen masu zabe.

 • Tun da sassafe jama’a suka fita

Tun da sanyin safiya jama’a a sassan Jihar Edo suka yi ta fita domin zuwa rumfunan zabe.

Jami’an zabe, da suka hada da masu yi wa kasa hidima da wakilan jam’iyyu da jami’an tsaro da masu sa ido sun yi cincirindo a cibiyoyin hukumar zabe (INEC) da ke Jihar Edo domin rabon kayan zabe da kai su rumfunan da za a gudanar da zaben da wuri.

Wasu jam’ina tsaro da wakilan jam’iyyu wata cibiyar aikin zaben na INEC.

Tuni dai kayan zaben suka fara isa rumfunan zabe.

Wani mai yi wa kasa hidima ya isa rumfar zabensa da kayan gudanar da zaben

Mista John Inadehi mai shekara 83 ya fito domin jefa kuri’a a garin BeninMista John Inadehi mai shekara 83 ya yi zabe fiye da sau 20.

Ya ce yanzu ma a shirke yake ya jefa kuri’arsa kuma ba shi da wata fargabar cewa za a yi murdiya.

“Ni dan birnin Benin ne kuma mu ba ma tashin hankali. Ina da kwarin gwiwar cewa za a gudanar da sahihin zabe,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu.


 • Ba za a bar mu a baya ba

Duk da rufe ayyuka da a aka yi domin gudanar da zaben, masu muhimman sana’oi, irin su Joy, mai sayar da abinci a babban titin Ring Road na birnin Benin, sun fito domin su jefi tsuntsu biyu da dutse guda.

Matashiya Joy mai sayar da abinci tana nuna katinta na zaben.

‘Yan kasuwa da ‘yan tireda sun rufe shagunansu kamar yadda hukumomi suka umarta a ranar zaben.

An rufe harkokin hada-hada a titin Ring Road na garin Benin.

Sallama!

Muna muku barka da safiya a wannan shafin da zai rika kawo muku abin da ke faruwa a zaben Gwamnan Jihar Edo na 19 ga Satumba, 2020 kai-tsaye.

Wakilanmu za su rika aiko da bayanai akai-aika domin ku san yadda ake ciki.

Dalibai masu koyon aikin jarida da Cibiyar Koyar da Binciken Kwakwaf a Aikin Jarida ta Premium Times (PTCIJ) ta horas domin kawo rahotannin zaben daga da Mazabun Majalisar Dattawa uku da ke jihar Edo za su mara wa wakilan namu baya.

Za ku iya amfani da maudu’an #EdoDecides, #EdoElects ko kuma #DTEdoGuber domin bin labarun zaben.

A kasance tare da mu.