Kusan mako hudu ke nan ana tataburza tsakanin Rasha da makwabciyarta Ukraine, lamarin da ya tilasta wa akalla mutum miliyan 10 tserewa daga garuruwansu a Ukraine.
Ga sabbin abubuwan da suka faru bayan kwana 26 da Rasha ta kaddamar da yaki a Ukriane.
- Kaso 75 na kasafin kudin Najeriya a rashawa yake karewa —Rahoto
- Ukraine na so a mayar da tattaunawarta da Rasha birnin Kudus
– Yoyon guba –
Gwamnan yankin Sumy na Ukraine, Dmytro Zhyvytsky, ya bukaci mazauna garin Novoselytsya da ke Arewacin kasar su nemi mafaka bayan wani kazamin fada ya haddasa yoyon sunadarin ammonia a wata masana’anta da ke kusa a garin.
– Ukraine ta yi fatali da wa’adin Rasha –
Rasha ta ba wa mazauna birnin Mariupol, wadda sojojinta suka yi wa kawanya wa’adin karfe 5.00 na safiyar Litinin 21 ga Maris, 2022 su mika wuya, tana barazanar gurfanar da wadanda suka ki mika wuya a gaban kotun soji.
Amma Mataimakin Fira Ministan Ukraine, Iryna Vereshchuk, ya fito a kafafen yada labarai ya yi fatali da wa’adin, da cewa “maganar mika wuya ga Rasha soki-burutsu ne”.
– Biden zai kai ziyara Turai –
Fadar White House ta Amurka ta ce Shugaba Joe Biden zai ziyarci nahiyar Turai ranar Juma’a domin ganawa da takwaransa na kasar Poland, Andrzej Duda.
– An yi wa fararen hula ruwan bama-bamai –
Ukraine ta zargi sojojin Rasha da yin luguden bama-bamai a wani kwalejin adabi da ke Mariupol, inda mata da kananan yara da wadansu mutum sama da 400 suke zaman mafaka.
– HIjkarfin da yaji –
Mahukunta birnin Mariupol sun zargin dakarun Rasha da kai wasu mazauna garin sama da mutum 1,000 Rasha karfi da yaji, suka kwace musu takardun fasfonsu na Ukraine. Hakan a cewarsu, laifin yaki ne.
– Hari a asibitin Chernigiv –
Magajin Garin Chernigiv, yankin da sojojin Rasha sun kashe fararen hula akalla 20 a luguden wutar da suka yi kan mai uwa da wabi bayan sun yi wa garin kawanya.
A cewarsa, “Muna cikin bala’i tare da matukar neman agajin gaggawa.”
– An tarwatsa cibiyar cinikayyar Kyiv –
Magajin Garin Kyiv, babban birnin Ukraine, ya ce akalla mutum daya ya rasu a sakamakon harbin makaman atilare da sojojin Rasha suka yi kan cibiyar cinikayyar birnin.
– ‘Ya kamata a zauna —Zelensky –
Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bukaci a gaggauta zama tsakanin kasarsa da Rasha.
Zelenskya ya bayyana cewa idan har za ta yiwu, to yin zaman a Isra’ila zai iya haifar da samakamon da ake bukata, wato zaman lafiya.
– An kusa sasantawa, inji Turkiyya –
Gwamnatin Turkiyya ta bayyana cewa ana samun nasara a tattaunawar sulhun da bangarorin biyu suke yi, har sun kusa kulla yarjejeniya.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Mevlut Cavusoglu, ya ce kasarsa a shirye take ta zama mai masaukin baki a ganawar da za a yi tsakanin Mista Zelenskyy da takwaransa na Rash, Vladimir Putin.
– Dawowar jakadanci –
Fira Ministan Slovenia, Janez Jansa, ya sanar cewa nan ba da jimawa ba jakadan kasarsa a Ukraine zai ci gaba da aiki a Kyiv.
Ya kuma yi kira ga sauran kasashen Turai da su yi hakan ganin cewa a halin yanzu Ukarine tana matukar bukatar huldar jakadanci ta kai-tsaye.
– Makamai masu gudun walkiya –
Rasha ta yi ikirarin harba makamai masu gudun walkiya wajen lalata wani rumbun mai a Kudancin Ukraine.
Sakataren Tsaron Amurka, Lloyd Austin, ya ce ko da hakan ya tabbata, babu wani sabon tasiri da zai yi a yakin.
– Ba ma ba wa Rasha Makamai —China –
Ofishin Jakadancin China a Amurka ya ce China ba ta taimaka wa Rasha da makamai domin yakar Ukraine; Amma bai kore yiwuwar yin hakan a nan gaba ba.
– Fafaroma ya yi tir da kisan gilla –
Fafaroma Francis ya yi Allah wadai da abin da ya kira “Kisan gilla na babu gaira, babu dalili da ake ta yi a kullum” a Ukraine.
Fafaroma Francis ya yi kira ga hukumomin duniya da su yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshe yakin, “Wanda babu dalilin yin shi.”
– Lalata masana’anar tama ta Azovstal –
Ukraine ta zargi sojojin Rasha da lalata masana’antar sarrafa tama ta Azovstal, wadda daya ce daga cikin manyan masana’antun sarrafa tama da nahiyar Turai ke tunkaho da su.
– Australia ta daina sayar wa Rasha aluminiyam –
Kasar Australia ta haramta fitar da aluminiyam da bauxite dinta zuwa Rasha, sannan ta bukaci a taimaka wa Ukraine da karin makamai da kayan jinkai.
Rasha dai ta togara ne a kan Australia domin samun kashi 20 cikin 100 na aluminiyam din da take bukata.
– ’Yan Ukraine miliyan 10 sun tsere –
Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutum miliyan 10 — fiye da rubu’in al’ummar Ukraine — sun tsere daga muhallansu sakamakon mamayar Rasha a kasar.
Hukumar ta ce zuwa ranar Lahadi, mutum miliyan 3.3 ne suka tsere daga Ukraine zuwa wasu kasashe domin samun mafaka.