✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wainar da aka toya a haduwar ‘karshe’ tsakanin Messi da Ronaldo

Ronaldo ya sha naushi a fuska.

A ranar Alhamis da ta gabata ce aka doka wasan sada zumunta tsakanin kungiyar kwallon kafa ta PSG da kuma gamayyar ’yan wasan kungiyar Al-Hilal da Al-Nassr masu buga gasar Saudi pro League.

Sabon dan wasan da Al-Nassr ta siya, Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye biyu a ragar PSG, a fafatawar da suka yi da babban abokin hamayyarsa Lionel Messi.

Messi ne ya soma jefa kwallo tun a minti na uku na wasan da aka yi tsakanin ’yan wasan hadakar na Al-Hilal da Al-Nassr da suka sha kashi da ci 4 da 5.

Ronaldo mai shekaru 37 ya zura kwallon farko a mintuna na 34 da soma wasa a bugun finareti kafin kara na biyu ana daf da tafiya hutun rabin lokaci, wanda shi ne wasansa na farko tun bayan da ya koma Saudiyya a yarjejeniyar da aka ce ta kai sama da Yuro miliyan 400.

Navas ya naushi Ronaldo a fuska

Mai tsaron ragar PSG, Keylor Navas ya naushi Ronaldo a fuska a kokarin dakile wani mummunar hari, lamarin ya sa alkali ya ba shi bugun fenareti wanda Ronaldo din ya zura a raga.

PSG

A bangaren PSG mallakin kasar Qatar, Messi da Kylian Mbappe duk sun zura kwallo a raga, yayin da Neymar ya baras da bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Daruruwan ’yan wasan kwallon kafa da hamshakan attajirai ne suka halarci wasan baje kolin a babban birnin kasar Saudiyya, wanda ya gudana makonni bayan da makwabciyarta Qatar ta kashe kudi a Gasar Kofin Duniya na farko a yankin Larabawa, wanda Messi na Argentina ya lashe.

Haduwar ‘karshe’ tsakanin Messi da Ronaldo

Masu ruwa da tsaki a fannin tamaula na hasashen wannan wasa dai shi ne na karshe da za a fafata tsakanin Ronaldo da Messi – ’yan wasa biyu mafi haskawa a duniyar kwallon kafa.

An yi hasashen ne la’akari da cewa Messi yanzu haka yana PSG a nahiyyar Turai, yayin da Ronaldo wanda ya koma murza leda a yankin Larabawa, babu wata gasa da za ta sake hada su filin tamaula guda.

Haka kuma, shekarun kowanne daya daga cikin ’yan wasan biyu sun doshi 40, saboda haka daf suke da su yi ritaya daga wannan sana’ar nishadantarwa mafi shura a doron kasa.

Wasan Bajakoli

Daga cikin mutanen da suka halarci filin wasa na Sarki Fahd mai kujeru 69,000, har da wani hamshakin attajiri dan kasar Saudiyya wanda ya biya dala miliyan 2.6 wajen sayen tikitin da ya ba shi damar shiga dakin sanya tufafi na ’yan wasan.

Wasan dai shi ne na farko da Ronaldo ya buga a Saudiyya Pro League, yayin da ake saran ya doka wa Al Nassr wasa a ranar Lahadi bayan ya sanya hannu kan yarjejeniyar kudi sama da Yuro miliyan 200, kamar yadda wata majiya ta kusa da kulob din ta bayyana.

Jakadan Saudiya

Majiyar ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa za a biya fitaccen dan wasan na Portugal karin Yuro miliyan 200, domin ya zama Jakadan Kasar Saudiyya da ake sa ran za ta karbi bakuncin Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2030 da hadin gwiwar Masar da Girka.