✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wai yin siyasar dole ne?

Idan na ce ni ba dan siyasa ba ne, wani na iya cewa ba gaskiya ba ce, domin kuwa ina hulda da ’yan siyasar ta…

Idan na ce ni ba dan siyasa ba ne, wani na iya cewa ba gaskiya ba ce, domin kuwa ina hulda da ’yan siyasar ta mabambantan hanyoyi. Wannan na iya zama gaskiya; sai dai da yake huldar ba ta tsaya ga dan siyasa ko kuma jam’iyya guda kurum ba, yana iya sa ra’ayin ya samu cikas. Hulda da ’yan siyasa dole ne a cikin tsarin rayuwar da muke ciki, idan ma mutum ya ce, shi bai da katin zama dan jam’iyya kaza ko kuma bai ra’ayin kowace jam’iyya, don haka a kai kasuwa, shi ba ruwansa, ina ganin wannan ba tunanin kwarai ba ne!

Duk dan Adam, a duk inda yake a doron kasa, yana tu’ammali da siyasa; ko dai a matsayin mai sha’awar wata jam’iyya ko kuma mai jefa kuri’a. Duk wanda ya ce zai koma gefe guda, wai ba ruwansa da siyasa to da alama zai ci kubeji. Ba yadda za a yi ka ce kai ba ruwanka da tsarin da dole sai ya shafe ka, (kai-tsaye ko a kaikaice), kana mai ra’ayinsa ko ba ka yi! Wannan haka yake, ba wai kawai a kasashen da suka ci gaba ta kowane irin fanni ba, har a cikin kasa irin tamu, inda  munafunci da cin amana da raggwanci da son kai suka yi kaka-gida a cikin tsarin gudanar da siyasar. Wannan shi ke sa wadansu ke ganin me zai hada su da jangwam din siyasa irin wannan, tunda ba a zuba abin kwarai a cikin tukunyar da ke bisa murhun siyasar ba.

Ga yawancin ’yan siyasar wannnan kasa, harkar siyasa tamkar tamola ce, ba wai wani abin da za a mayar da hankali ba ne, tamkar addini ko akida da za ta gudanar da rayuwa. Yadda ’yan siyasarmu ke kallon tsarin siyasar bai wuce yadda masu ra’ayin kwallon kafa, musamman irin ta Ingila (ko Turai) ke faman yi ba. A dai buga kwallo, a yi dariya, a yi annashuwa, a kwashi awalaja, a nufi banki!

Ga yawancin ’yan siyasarmu, ana yin siyasar ce domin a hau mulki, a samu mukami, a yi ta wandaka da nuna isa. Wadansu na shiga harkar siyasar ce domin kurum a ci zabe ta kowace irin hanya, mai kyau ko marar kyau!

Ina fadar haka ne ba wai don ban ga abin a-zo-a-gani game da siyasa ba, ko alama. Amma kullum tunanina shi ne, me ya sa siyasar wadansu ke da armashi da taimaka wa al’umma, amma tamu kullum sai madalla-tir! Ka duba ka gani, shin mene ne abin burgewa game da tsarin siyasarmu? Shin jam’iyyun siyasar ne ko masu shugabancin jam’iyyun ko kuwa mabiyan jam’iyyun siyasun? Idan jam’iyyun siyasun ne, me ya bambanta su a manufa da tsari? Idan kuwa shugabannin ne, me ya bambanta na waccan jam’iyya da waccan? Me ya sa yau za ka shugaba ko jami’i ko kusa a wata jam’iyya, ya bar tasa jam’iyya, wai da magoya bayansa ya koma wata? Wani ma sai an sha gwagwarmaya, an kai-ruwa-rana, a zabe shi a bisa wani matsayi, sai ya watsar da tasa jam’iyya ya koma wata, a kuma zauna lumui! Me ya bambanta kudirorin wannan jam’iyya da waccan? Leka ofisoshin jam’iyyun siyasun da muke da su ka nemi a ba ka manufofinsu da kudirorinsu, idan ka kwatanta za ka ga ba wani bambanci, tamkar danjuma ne da danjummai!

Ba wannan kadai ba, idan ka natsu da kyau za ka ga cewa, ba wani shiri da jam’iyyun siyasun suka yi na ciyar da kasa gaba. Babban shirin kowace jam’iyya shi ne ta ci zabe, me za ta yi bayan zabe, ba ruwanta balle kai kuma da ka zabe ta. Tsarin siyasarmu abin da ya gada shi ne, a tabbata an ci zabe, a hau karagar mulki, a shiga bayar da kwangila.

Wannan shi ne tsarin siyasarmu! Hakan ne kuma domin da zarar aka ci zabe ba a batun komai sai rarraba mukamai da tantan da dukiyar jama’a. Nan da nan sai ka ga dan siyasar da ba kowan kowa ba kafin zabe da manyan motoci da gidaje da milyoyi kudi a banki; gida da waje. Ya zama wani hamshakin mai kudi, kana ta mamakin inda ya samu wannan dukiya!

Ba wai ina nufin cewa dukan jam’iyyun siyasu ko ’yan siyasar haka suke ba, amma bisa kiyasi yawancin jam’iyyun siyasun da ’yan siyasar duk haka suke. Babbar manufarsu da jam’iyyunsu ita ce a ci zabe, a shiga bushasha da dukiyar talakawa. Wasunsu kuma ba abin da suka sa gaba illa dawwama bisa mulki. Su ne za ka ji suna fadar; mun yi mulki a zamanin su Sardauna da mu aka caba a zamanin Gowon, ko a zamanin da Shagari ya hau da mu aka dama, haka zamanin Babangida da Abacha. Shi kuwa Obasanjo dole ya yi da mu, balle ’Yar’aduwa da Jonathan. Yanzu kuma Buharin dole yake yi da mu. Idan kuma ba mu a doron kasa nan da shekaru masu zuwa da kannenmu ko ’ya’yanmu za a yi siyasar, ko ana so, ko ba a so!

Shi ya sa siyasar gado da barna da baba-kere da cin hanci da sata a fili ba za ta taba barin ruhin rayuwarmu ba! Ba kuma abin da kai ko ni ko shi ko ita ko su da ke faman shan rana da sanyi da yunwa da fatara wajen ‘zabensu’ za mu iya yi! Shi ya sa idan suna cika baki, suna yi mana yanga da zazzare idanu kamar su ne iyayen gijinmu, ba wani abu da za mu iya yi, idan wai muna jin cewa da bazarmu suke rawa! Suna yin kememe ne wata sa’a saboda sun fi mu gaskiya, ba da bazarmu suke rawa din ba, domin kuwa sun saya, sun biya! Ta yaya wanda ya mika wuya saboda Naira 200 da aka ba shi, ya yarda ya mika ’yancinsa, zai iya cewa uffan ga wanda ya kame mulki ta hayewa doron bayansa. Me zai iya cewa tunda ya sayar da ’yancinsa? Ko kana da mafita ga irin wannan mutum? Na sa a mala!