✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wahalar man fetur ta sake kunno kai a Abuja

Sai dai har yanzu NNPC bai magantu ba a kan matsalar

Gidajen man fetur da dama a Babban Birnin Tarayya Abuja sun rufe bayan wahalar man fetur ta sake kunno kai.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito yadda ake ci gaba da samun dogayen layuka na masu sayen man fetur a birnin.

A wani zagaye da wakilin NAN ya yi a unguwannin Wuse da Gwarimpa da Wuye da Kubwa ya gano yadda ake fama da matsanancin layin man, inda akasarin gidajen man ba sa sayar wa masu ababen hawa.

Wani da ya zanta da wakilinmu mai suna Alex Udoh, ya ce an fara samun layukan ne tun a ranar Asabar din da ta gabata wanda shi ma da kansa ya yi kokarin ganin ya samu sayen man amma hakansa ya ci tura.

Mista Alex ya yi kira ga gwamnati da sauran hukumomi da su samar da sahihiyar mafita kan karancin mai da ake fama da shi saboda irin tasirinsa ga tattalin arziki.

Shi ma wani direban Tasi mai suna Malam Yakubu Umar ya ce ya kai kimanin awa biyar a kan layin.

A cewarsa, “Jiya ma na sayi man ne daga hannun ’yan bumburutu wanda hakan ya sa a aikin nawa ban samu wata riba ba.”

Har yanzu dai Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) bai bayyana dalilin karancin man fetur ba da ma irin matakan da yake dauka domin shawo kan matsalar.

A ’yan watannin baya dai an sha fama da wahalaran fetur a kusan ilahirin biranen Najeriya, inda ’yan bumburutu suka rika cin karensu ba babbaka.