Matsalar karancin man fetur da aka sha fama da ita na tsawon watanni a Jihar Kano, ta fara ja baya.
Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewar yanayin layuka a gidajen mai ya fara raguwa yayin da ake ci gaba da samun wadataccen mai a Jihar.
- Bashin da ake bin Najeriya ya karu zuwa N46.25tr —DMO
- An kama matashin da ake zargi da yi wa jaririyar wata 9 fyade a Legas
NAN ya ruwaito cewar har yanzu gidajen mai a jihar na ci gaba da sayar da man fetur a kan Naira 210 kan kowace lita.
Sai dai wasu gidajen man sun bude a Jihar, amma ba sa sayar da man.
Wani mai abun hawa a jihar mai suna Malam Bala Ado, ya ce ya shafe tsawon minti 15 a gidan man Aliko amma bai samu damar shan man ba sakamakon layi da yake bi.
“Na ji dadin ci gaban da aka samu idan aka kwatanta da na makonnin da suka wuce,” in ji shi.
Ya bayyana cewar gidan man na sayar da kowace lita a kan Naira 210.
Ado ya roki gwamnati ta kawo karshen wahalar da ’yan kasuwa suka jefa mutane a ciki game da tsadar man fetur din.
Shi kuwa Alhaji Sani Musa, cewa ya yi kada da minti 15 ya shafe kafin ya sha mai a gidan man AA Rano.
Matsalar karancin mai dai ta shafe watanni ana fama da ita, inda aka dinga yin kwan-gaba-kwan-baya tsakanin Gwamnatin Tarayya da kuma ‘yan kasuwa.