✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wahalar man fetur: Galan ya kai N2,000 a wajen ’yan bumburutu a Kaduna

Yanzu haka a Kaduna ’yan bumburutu ke cin karensu ba babbaka.

Yayin da wahalar man fetur ke ci gaba da kamari a biranen Najeriya, Aminiya ta gano cewa yanzu haka a birnin Kaduna, farashin galan daya na man ya kai N2,000 a hannun ’yan bumburutu.

Aminiya ta gano akasarin masu ababen hawa na kwashe sa’o’i a kan layi suna jiran sayen man fetur, wanda hakan ya sa yan bunburutun ke cin karensu ba babbaka.

Kazalika, masu motocin haya su ma sun kara nasu farashin wanda hakan ya kara jefa jama’a cikin wahala.

Wasu daga cikin mutanen da Aminiya ta zanta da su sun bayyana rashin jin dadinsu da karancin man da ake fama da shi.

Umar Ramalan, mazaunin unguwar Badarawa ya ce suna wahala wurin kai yara makaranta da safe saboda rashin motocin haya.

“Yanzu sun kara mana kudin mota daga N100 zuwa N150 daga Badarawa zuwa cikin gari. Sannan kuma samun motar da zaka shiga ne matsalar kasancewar sun yi karanci akan hanya,” inji shi.

Shi ma Salisu Suleiman, wanda direba ne a Kaduna ya ce, “Gaskiya babu dadi sai dai kurum mu yi addu’ar samun sauki domin karancin man fetur ai akwai matsala.”

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa akasarin gidajen man fetur da ke jihar basu da mai, kuma kadan daga cikin gidajen da ke sayar da ma sune Mubil da ke kan titin Muhammadu Buhari sai kuma gidan man AYM Shafa da ke akan titin Ali Akilu.

Wakilin namu ya kuma lura cewa ’yan bumburutun kadai ke cin karensu ba babbaka a yanayin, inda suke kara kudi a duk lokacin da suka ga dama.

Musa Adamu, direban motar haya kira yayi ga gwamnati da ta kawo masu dauki ta hanyar kawar da da gurbataccen man fetur da aka ce an shigo da shi kasar nan.