Hukumar Shirya Jarabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta saki sakamakon jarabawar kammala sakandire ta shekarar 2021.
Shugaban hukumar a Najeriya, Mista Patrick Areghan, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Litinin.
- Mutum biyar da ka iya maye gurbin Solskjaer a Manchester United
- Ana fama da karancin kwaroron roba a Kenya
A cewarsa, jimlar dalibai 1,573,849 ne suka yi rajistar jarabawar a cibiyoyi 19,425 da hukumar ta amince da su a fadin kasar nan, inda daga ciki kuma 1,560,261 suka zana jarabawar a bana.
Sanarwar ta ce akalla dalibai 1,274,784 ne suka sami nasara a darusa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.
Ya kuma ce hukumar ta rike sakamakon dalibai kimanin 170,146 da ta samu da laifukan satar jarabawa.
Kazalika, sanarwar ta ce tuni hukumar ta fitar da sakamakon dalibai 1,256,990, kimanin kaso 80.56 cikin 100 na daliban da suka zana jarabawar a Najeriya a bana.
Patrick ya kuma ce suna nan suna kokarin fitar da sakamakon ragowar daliban, wadanda ya ce wasu matsalolin da suka samu da wasu daga cikin darusan da suka zana ne suka haifar musu da tsaikon.
Hukumar dai ta ce lambobin sirrin da za a yi amfani da su wajen duba sakamakon jarabawar na nan a jikin katin da suka yi amfani da shi wajen rubuta jarabawar.
Sanarwar ta kuma ce jarabawar, wacce aka shafe sati bakwai ana yi a bana dai ta yi fama da matsalolin tsaro a sassa daban-daban na kasar nan.