Gwamnatin Tarayya ta ce makarantun sakandare a Najeriya za su rubuta jarabawar WAEC daga ranar biyar zuwa 14 ga watan Satumbar 2020.
Ministan a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana hakan ranar Litinin a yayin amsa tambayoyi a jawabin hadin gwiwa da kwamitin kar-ta-kwana mai yaki da cutar COVID-19 ya yi a Abuja.
A cewarsa, kasashen da ke amfani da harshen turancin Ingilishi (Najeriya, Ghana, Saliyo, Gambiya da Laberiya) su ke rubuta darussa iri daya za su gudanar da jarabawar kamar yadda aka tsara tun da farko.
Ya ce dukkan kwamishinonin ilimi da gwamnonin jihohi sun amince za a sake bude makarantu daga ranar 4 ga watan Agusta a shirye-shiryensu na fara jarrabawar daga ranar 17 ga watan na Agusta.
Ministan ya ce, “Mun cimma yarjejeniyar ci gaba da jarabawar kamar yadda aka amince tun da farko a jadawalin jarrabawar, sai dai darussan da suka shafi Najeriya ita kadai za su gudana ne daga biyar zuwa 14 ga watan Satumba.
“Za a yi jarrabawar ne bai daya a dukkan kasashe daga ranar 17 ga wata kamar yadda aka amince tun da farko. Kowacce jiha a Najeriya ta amince da haka kuma za a fara yi wa dalibai bita”, da zarar an bude makarantun inji ministan.
Ya ce an yi hakan ne domin a ba daliban aji uku na babbar sakandaren damar su shirya a tsanake kafin fara jarabawar.