Jihar Jihar Kano ta ayyana cibiyoyi 12 na jarabawar kammala karatun sakanadare ta WAEC ga daliban makarantunta ma kwana 33.
Hukumar Kula da Makarantun Sakandare ta Jihar Kano (KSSSMB) ta ce hakan zai hana yada cutar COVID-19 a lokacin jarabawar da za a fara daga ranar 17 ga Agusta, 2020.
Babban Sakataren KSSSMB Bello Shehu, ya ce daliban sakandaren gwanmati ta GGUC Kachako da GGSS Sumaila da GGSS Albasu za su yi jarabawar a GGUC Kachako.
GGC Kano kuma ita ce cibiyar da aka ware wa daliban GGSS Kura da GGSS Madobi da kuma GGC Kano.
GGASS Danbatta da GGASS Tudun Wada za su yi tasu a GGAG Goron Dutse. ‘Yan GGSS Kwa kuma za a GGC Dala.
Na GGSS ‘Yar Gaya da GGSS Kabo za su yi a GSS Shekara, an kuma ware GGSS Jogana ga daliban GGC Gezawa da GGSS Jambaki.
“GSS Kafin Mai-Yaki, GC Tudun Wada da GSS za su yi tasu jarabawar a makaranatar sakandaren gwamnati da ke Karaye.
“GSS Rano da GASS Tsangaya da GSS Ajingi kuma makarantar GSS Sumaila za su yi tasu”, inji shi.
Shehu ya ce sauran cibiyoyin su ne GSS Danbatta domin daliban GSS Bichi da GSS Bagwai da kuma GSCS Wudil. Daliban GSS Dawakin Tofa kuma za su yi tasu a GSS Gwarzo.
‘Yan GSS Tudun Maliki da Kwalejin Chinese Bilingual kuma kowannensu za su rubuta jarabawar ne a makarantunsu.
Haka kuma daliban sauran makarantun gwamnati guda 161 da ke fadin jihar za su yi jarabawar ne a makarantunsu.
Ya bukaci iyaye su tabbata ‘ya’yansu sun koma kamaranta a kan kari a ranar Lahadi 9 ga Agusta 2020, kamar yadda gwamnain jihar ta sanya wa daliban ajin karshe na makarantun kwana.
Dalibai 11,000 ne za su rubuta jarabawrar WAEC a jihar Kano, inda daliban za su ci gaba da karatu a ranar Litinin 10 ga Agusta, 2020.