✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wadda ta yi kutse a shafin Hisbah ta bayyana kanta

Matashiyar ta ce sun gano yadda Hisbah ke amfani da shafin nasu wajen kallon fina-finan batsa.

Wata matashiya ’yar Najeriya ta bayyana kanta a matsayin wadda ta yi kutse a shafin Facebook na Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.

Aminiya ta ruwaito yadda, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya sanar da yadda aka yi shafin hukumar kutse, inda ya roƙi jama’a su taimaka wajen dawo da shafin.

Ya kuma bayyana cewa hukumar ta tuntuɓi kamfanin Meta, don taimaka musu kan yadda za su dawo da shafin daga hannun waɗanda suka yi musu kutse.

Shugaban Sashen Kimiyya da Fasaha na Hisbah, Sani Zailani, ya bayyana cewa an taɓa yi wa asusun kutse a baya kuma Meta ta yi alƙawarin magance matsalar cikin sa’o’i 48.

Shafin Facebook na matashiyar da ta yi iƙirarin kutse a shafin Hisbah
Shafin Facebook na matashiyar da ta yi iƙirarin kutse a shafin Hisbah

Sai dai, bayan sa’o’i 72 da yin kutsen, wata mai amfani da Facebook mai suna Mariam Oyiza Aliyu, ta ce ita ce ta yi wa shafin hukumar kutse.

Oyiza, wadda ta ke da mabiyan 13,000 a Facebook, ta bayyana kanta a matsayin mai kare haƙƙin ɗan Adam, tsohuwar Musulma kuma mai goyon bayan mata.

Bayanan da ta ɗora a shafinta, sun nuna cewa ita ‘yar asalin garin Okene ce, da ke Jihar Kogi, amma bayananta sun nuna yanzu haka tana zaune a yankin Leeuwarden, Friesland da ke ƙasar Netherlands.

Oyiza, ta ce ta yi kutse ne a shafin Hisbah a matsayin martani ga abin da ta kira “cin mutuncin mata” da hukumar ke yi.

Ta wallafa a shafinta cewa, “Barkanku da safiya jama’a, na kawo muku labari mai daɗi. Hukumar Hisbah ta Kano, waɗanda ake ganinsu da ƙima da kuma masu bayar da tarbiyya, sun shiga wani shafin batsa da wasu masu kutse suka wallafa kwanakin baya. To, yanzu mun tona asirin munafukai.”

Kazalika, matashiyar ta buƙaci Hisbah ta nemi gafarar matan da ta ci zarafinsu tare da ba su diyyar Naira 500,000 kowannensu kafin ta saki shafin nasu.

Sai dai Aminiya ba tabbatar da ikirarin matashiyar ba.

Ko da aka tuntuɓi shugaban sashen fasaha na Hisbah, Sani Zailani, ya ce ba shi da masaniya kan buƙatar matashiyar.

“Ba mu ga sakon wannan mata ba, amma za mu duba lamarin kuma za mu ɗauki matakin da ya dace,” in ji shi.