✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wadansu daraktoci a Jigawa ba su iya rubuta rahoto ba

An gano cewa wadansu manyan daraktoci a Jihar Jigawa da dama da ba su iya rubuta rahoto ko bayanin da ya shafi al’amuran aikin ofis…

An gano cewa wadansu manyan daraktoci a Jihar Jigawa da dama da ba su iya rubuta rahoto ko bayanin da ya shafi al’amuran aikin ofis ba, wanda haka ya sanya Shugaban Ma’aikata na Jihar, Alhaji Muhammad Inuwa Tahir ya shirya wa daraktocin bita domin koyar da su yadda za su rika wadannan rubuce-rubuce da suka shafi aiki.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugaban Ma’aikata, a yayin horar da daraktocin a dakin taro na Hukumar Horar da Ma’aikata da ke Dutse, wanda ya gudana a ranar Talatar da ta gabata.
Ya ce ofishinsa ya shirya bitar ce domin tunatar da ma’aikatan yadda ake rubuta irin wadannan muhimman bayanai na aikin ofis. Ya ce, wani abin takaici da suka gano shi ne, da dama daga cikin daraktocin ba su iya shirya bayanai ko rubuta takardar memo ba. Ya kara da cewa, a yayin bitar ne za a gwada musu dabarun tsara wadancan abubuwa da suka shafi aikin ofis, domin ganin an inganta aikin gwamnati a jihar. Ya hore su da su tsaya tsayin-daka wajen koyon yadda ake wadannan rubuce-rubuce.
A cewar shugaban ma’aikatan, ta yin haka ne gwamnatin jihar za ta samu managartan ma’aikata a jihar, masu kwazo kamar yadda ake da bukata. Ya kara da cewa sun tantance ma’aikata a gaba dayan jihar, saboda an dade ba a dauki ma’aikata ba a jihar; dalili ke nan aka samu rauni wajen aikin gwamnati a jihar.
Ya kara bayani cewa, a yanzu haka gwamnatin jihar ta hada kai da Jami’ar Bayaro da ke Kano da Jami’ar Jos, wadanda za su rika horar da ma’aikatan jihar da suka mallaki takardun shaidar karatu na Diploma da NCE, yadda za a rika ba su guraben karatun digiri. Ya ce a tsarin, shekara biyu kadai za su yi suna karatu, kafin su samu  digirin.