✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Wadanne shugabannin duniya aka gayyata bikin binne Sarauniya Elizabeth II?

Wadanda za su halarta sun hada da sarakunan gargajiya da Shugabannin kasashe

Daruruwan shugabanni da masu rike da sarautun gargajiya daga sassa daban-daban na duniya ne ake sa ran za su halarci bikin binne sarauniya Elizabeth II da zai gudana ranar Litinin a birnin Landan na Birtaniya.

Bikin dai an yi ittfikafin shi ne irinsa da zai fi hada shugabannin duniya a tsawon shekaru masu yawa.

Za dai a binne ta ne a Westminster Abbey da ke Landan, wanda yake da fadin cin kusan mutum 2,000, kuma shugabannin kasashe kusan da wakilansu kimanin 500 ne ake sa ran za su halarta, kafar yada labarai ta BBC ta rawaito.

Kazalika, iyalan marigayiya Sarauniyar da kawayenta da abokan arziki da sauran manyan mutane da ’yan siyasar Birtaniya ma za su halarta.

Aminiya ta zakulo muku jerin fitattun shugabannin da aka gayyata wajen bikin daga Shugabannin Kasashe ko Firaministoci da sarakunan gargajiya da kuma ma wadanda ba a gayyata ba.

Ga wasu daga cikinsu:

Sarakunan gargajiyar da aka gayyata

 • Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman,
 • Galibin sarakunan gargajiyar da ke Tarayyar Turai za su halarta
 • Basaraken Japan, Naruhito da mai dakinsa, Empress Masako
 • Sarkin Holland, Willem-Alexander
 • Sarauniya Maxima da Gimbiya Beatrix
 • Sarki Philippe na Belgium
 • Sarki Harald V na Norway
 • Yarima Albert II na Monaco
 • Sarauniyar Denmark, Margrethe
 • Sarkin Spain, Felipe VI da mai dakinsa, Letizia

Shugabannin Kasashen duniya

 • Shugaban Amurka, Joe Biden da matarsa,
 • Matar Shugaban Ukraine, Olena, Volodymyr Zelensky
 • Shugaban Faransa, Emmanuel Macron
 • Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan
 • Shugaban Brazil, Jair Bolsonaro
 • Mataimakin Shugaban Kasar China, Wang Qisha
 • Shugabar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen
 • Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Charles Michel
 • Shugaban Italiya, Sergio Mattarella of Italy
 • Ministan Harkokin Wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier
 • Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Isaac Herzog
 • Ministan Harkokin Wajen Koriya ta Kudu, Yoon Suk-yeol
 • Firaministan Arewacin Ireland, Micheal Martin
 • Firaministan Kanda, Justin Trudeau,
 • Firaministan Australiya, Anthony Albanese
 • Firaministan New Zealand, Jacinda Ardern
 • Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo
 • Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa
 • Firaministan Bangladesh, Sheikh Hasina,
 • Shugaban Sri Lankan, Ranil Wickremesinghe
 • Firaministan Fiji, Frank Bainimarama

Wadanda ba a gayyata ba

 • Shugaban Rasha, Vladimir Putin
 • Shugaban Iran,
 • Shugaban Nicaragua
 • Shugaban Koriya ta Arewa
 • Shugaban Belarus
 • Gwamnatin Taliban ta Afghanistan
 • Shugabannin kasashen Myanmar da Siriya da Venezuela

(AFP)