’Yan sanda a Jihar Legas sun yi nasarar kubutar da wata yarinya ’yar shekara biyu da aka sace a wani coci a Tsibirin Wuta da ke Unguwar Agege a Legas.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Legas, DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa, wadanda ake zargi da sace yarinyar sun yi garkuwa da ita ce a Unguwar Igando inda suka nemi iyayenta su biya kudin fansa. “Sai suka yi ta sauya wajen da za a biya su kudin fansar har sau hudu a yankin Unguwar Igando lamarin da ya sanya jami’anmu da ke yankin suka yi masu kofar rago suka kama su,” inji shi.
Ya ce, wadanda ake zargin sun hadar da Nwaigbo Magnus da Sidtus Osunwoke Egwim, kuma tuni an mika yarinyar mai suna Esther Ojo ga iyayenta. Ya ce, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Legas, Zubairu Mu’azu ya ba da umarnin ci gaban da bincikar wadanda ake zargin za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike a kansu.