Wadanda suka yi garkuwa da wasu limaman cocin Methodist a Jihar Abiya sun bukaci a biya su Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa kafin su sake su.
Mutanen dai sun sace babban limamin Kirista kuma jagoran cocin, Samuel Kanu-Uche tare da wasu limaman mujami’ar da aka yi garkuwa da su tare.
- 2023: Atiku ya fara bin ’yan takarar da ya kayar a PDP gida-gida
- Tashin ‘bam’ a mashaya ya jikkata mutum 11 a Kogi
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa, an yi garkuwa da wadanda lamarin ya shafa ne a kan hanyarsu ta dawowa daga wani taro da suka halarta a Lahadin da ta gabata a yankin Karamar Hukumar Umunneochi ta Jihar Abiya.
Sakataren cocin, Rabaran Michael Akinwale ne ya shaida wa manema labarai kudin fansar da maharan suka nema cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Litinin.
Don haka ya yi kira ga daukacin mambobin cocin tasu da su taimaka a yi karo-karo don hada kudin da ake bukata wajen kubutar da wadanda aka sacen.
Akinwale ya ce wannan jarrabawa ce wadda majami’arsu za ta kai kukanta ga Ubangiji don samun mafita.
Tuni dai Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Abia, SP Geoffrey Ogbonna, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Lahadi.
Ya ce, “Abin takaici ne, amma ana ci gaba da kokarin ganin an ceto wadanda lamarin ya shafa.
“Muna bukatar jama’a su taimaka mana da muhimman bayanan da za su jagorance mu zuwa ga kabutar da su,” inji Ogbonna. (NAN)