Ana zargin wasu bata-gari su biyar sun hallaka wani mutum da mai dakinsa ta rasu kasa da wata guda da suka gabata sakamakon hadarin mota a Imo.
Mutumin mai shekaru 47 mai suna Wisdom Mbakwe, ya rasa ransa ne yayin da yake tsaka da shirye-shiryen jana’izar binne mai dakin nasa.
- Na Je Amurka, An Ba Ni Aiki Saboda Harkar Wasanni —Salma Sports
- Ba Za Mu Sake Amincewa Da Inkonkulusib Ba A Kano —Abba Gida-Gida
Margayiyar wacce ’yar asalin kasar Guinea ce, ta gamu da ajalinta ne ranar 11 ga watan Satumba, a kan hanyarta ta zuwa kasuwa.
A ganawar wakilinmu da ’yar uwar margayin mai suna Chinyere Ajonu, ta ce sun samu labarin kisan ne daga bakin wani yaro da lamarin ya faru kan idonsa.
“Ya ce da karfe 6:01 na safe ne ya bude kofar gidan don ya yi sharar tsakar gida kamar yadda ya saba, sai ya bar kofar a bude, don ya je ya dauko madebin shara.
“A lokacin ya ce marigayin na ta addu’o’insa da ya saba, kawai sai ya ji ya yi ihun Yahweh, Yahwe.
“Daga nan ne ya ruga don ya ga me ke faruwa, sai ya ga marigayin na kokawa da wasu mutane biyar da ke kokarin saran sa da adda.
“Sai ya ruga a waje don neman agajin ’yan unguwa, amma kafin su zo har an kashe shi da sara, an lullube shi da labulen dakin.
“Duk bayan mun taru an yi cirko-cirko kuma sai wani dan acaba ya zo ya ce yana zargin su ya sauke a wani wuri, saboda ganin taruwar mutane a kofar gidan ya sa suka ce masa ya kara sauri, abin da ya sa ya fara zargin su ke nan.
“Daga na kuwa muka bi su, aka kamo su wasu ko takalmi babu a kafarsu saboda sauri”, in ji ta.
Kakain rundunar ’yan sandan jihar, CSP Mike Abbtam, ya tabbatar da kamo wadanda ake zargin, sai dai ya ce suna ci gaba da baincike kafin maka su a kotu.