Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar da karin mutum takwas da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.
Wannan ya sa adadin mutanen da zuwa yanzu aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 89.
An samu karin mutane bakwai a jihar Legas, hakan ya sa Legas ke da adadin mutum 59 da suka kamu da cutar a Najeriya kuma su ke da mafi yawan masu cutar a kasar. Sai kuma guda a Jihar Benuwe.
Hakan ya sa adadin mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya ya kai 89.
8 new cases of #COVID19 have been reported in Nigeria, 7 in Lagos and 1 in Benue State.
As at 04:00 pm 28th March there are 89 confirmed cases of #COVID19 reported in Nigeria with 1 death. pic.twitter.com/kbL7yIMiLs
— NCDC (@NCDCgov) March 28, 2020
Jerin jihohin Najeriya da cutar Coronavirus ta bulla da kuma yawan mutanen da cutar ta kama:
Legas- 59
Abuja- 14
Ogun- 3
Enugu- 2
Ekiti- 1
Oyo- 3
Edo- 2
Bauchi- 2
Osun-1
Rivers-1
Benuwe- 1